Labarai

Mutane 4 da za su yi sulhu a tsakanin Sarki Sanusi da Ganduje

Fadar shugaban kasa ta kafa kwamitin mutane hudu da za su kawo karshen takun saka wajen tabbatar da sulhu a tsakanin Sarkin Kano Mai Martaba Muhammadu Sanusi II da kuma gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje.

Fadar shugaban kasa dake garin Abuja ta gayyaci shugabannin biyu a ranar Juma’ar da ta gabata domin neman sulhun ta su kamar yadda kafofin wata labarai na kasar nan da dama suka wassafa.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, kwamitin mutane hudu da fadar shugaban kasa ta kafa domin warware gabar dake tsakanin Gwamna Ganduje da kuma Sarkin Kano sun hadar da gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi a matsayin jagora.

Sauran ‘yan kwamitin sun hadar da gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi da kuma takwaran sa na jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar.

Ana iya tuna cewa gwamnatin jihar Kano ta bukaci Mai Martaba Sarki Sanusi da ya bayyana yadda aka waye gari babu kimanin Naira biliyan 3.4 a asusun fadar Kano. Sai dai fadar yayin mayar da martani ta ce abin da ta riska a asusunta bai wuci Naira biliyan 1.89.

KARANTA KUMA:

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, al’ummar jihar Kano sun bayyana mafi kololuwar farin cikin su yayin da aka samu sulhu a tsakanin Gwamna Ganduje da kuma Sarki Sanusi inda a cewar su hakan shi zai tabbatar da dorewar zaman lafiya da kuma ci gaba a jihar.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button