Sunday, 16 June 2019
Matsanancin zafin Rana ya tilasta jama'a zaman gida a kasar Kuwait (Kalli Hotuna)

Home Matsanancin zafin Rana ya tilasta jama'a zaman gida a kasar Kuwait (Kalli Hotuna)
Ku Tura A Social Media


Daga Haji Shehu

Zurga-zurgar ababen hawa ya tsaya cak a kasar Kuwait sakamakon matsanancin zafin rana wanda masana suka bayyana cewar a tarihin duniya ba a taba samun irin sa ba.

Zafin Ranar mai maki 63°C a ma'aunin Selshiyos, ya daddage robobi da tayoyin mototin da aka ajiye a bakin tituna, ya kuma haddasa konewar wasu ababen hawan dake fake a bakin wasu manyan hanyoyi.

Jaridar Al-Qabas ta nakalto cewar zafin ranar ya kone dayawa daga cikin robobin wutar bada izinin tafiya ga ababen hawa, sannan ya hana jama'a fitowa daga gidajen su na tsawon awanni.

Majiyar tace Sakamakon wannan matsanancin zafin Rana, jama'a kan kauracewa fita waje daga karfe 12 na safe har zuwa karfe 4 na yammaci.Share this


Author: verified_user

0 Comments: