Sunday, 16 June 2019
Matashi yayiwa Matarsa Kishiya Da Babbar Aminiyatar A Duniya

Home Matashi yayiwa Matarsa Kishiya Da Babbar Aminiyatar A Duniya
Ku Tura A Social Media


Ta taya Mai-gidanta murna bayan ya auri wata Aminiyarta
Mun samu labari cewa wani Balarabe ya auri wata daga cikin manyan Aminan Mai dakinsa domin ta zama Matarsa ta biyu.

 Wannan aure da wannan Bawan Allah ya yi, ya jawo magana daga jama’a. Kamar yadda mu ka samu labari, Matar wannan mutumi da aka yi wa kishiya ita ce ta rika yada labari da kan ta. Wannan Mata da ake kira Umm Abdullah, ita ta bada labarin mijin ta ya sake aure.


 ta bayyana auren Maigidan na ta ne a shafin ta na sada zumunta na Instagram. Matar ta nuna cewa duk da wannan aure, ta na kaunar Mijin na ta da kuma wannan Aminiyar ta. Mutane da-dama dai musamman ‘yan mata wanda ba su sha’awar kishiya a gidan aure, sun nuna cewa wannan aure bai burge su ba. Wannan Larabawa dai duk su na zaman lafiya da junansu.

Wannan Mata ta ke cewa sun rasa gane wanda Mai gidan na su ya fi kauna a cikinsu domin kuwa duk ya kan fada masu kalamai iri daya ne a lokacin da ya zauna da ita da kuma kishiyarta.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: