Thursday, 27 June 2019
Maganin Da Shawara Ga Wadan Da Suka Daina Istiba'i Wato (Masturbation)

Home Maganin Da Shawara Ga Wadan Da Suka Daina Istiba'i Wato (Masturbation)
Ku Tura A Social Media


 To Alhamdulillah kamar yadda nayi Alkawari zan kawo magani wanda wadan da suka tuba ga aikata wannan abu za suyi amfani da shi,to gashi yanxu insha Allah zan cika hadi da shawarwari.

Da farko duk wanda ya tsinci kansa a irin wannan hali kuma ya gane babu kyau ya kuma fahimci illolin sa to abinda zai fari yi shine ya daina aikata wannan abu kwatakwata, ma'ana ya bar aikata shi.

Na biyu kuma ya tuba ga Allah domin Allah a kullum mai rahma ne ga bayin sa kuma mai jinkai a gare su.kuma yayi Alkawarin bazai sake aikata shi ba,har izuwa karshen rayuwar sa.

Na uku shine daina kusantar dukkan wani abu da yake tayar maka da sha'awar ka,kamar kallon photonan banza,kallon finafinan banza koda irin Nigerian film ne indai yana mutsar da sha'awar ka to dole ne ka daina,sannan yawan mu'amala da matan da ba muharraman ka ba,da yawan zancin fasikan ci tsakanin ka da wata,koda kuwa matar daza aura ce.

Na hudu ka yawai istigfari da hailala da salatin Annabi Sallallahu alaihi Wasallama,da yawaita karatun Alqur'ani da yawaita nafilfili.
Abu na 5 kuma shine yin amfani da magani wanda zai dawo maka da abubuwan da ka rasa a wanchan lokacin.

ABINDA ZA'A NEMA

1. Garin habbatussauda
2. Garin haltit
3. Garin Kusdul hindi
4. Garin Albabunaj
5. Garin Tafarnuwa.
6. Zuma

Da farko Zaka hada Wadan nan kowanne kamar chokali 10 sai ka hade su waje daya ka samu Zuma kamar kofi biyu ka zuba garin duka a ciki ka hada ka gauraye su ka cakuda sosai ya zama zumar sa garin sun zama daya,

Sai ka ajiye ka rika shan chokali 3 sau 3 a rana har na tsawon wata 1.

HANYA TA BIYU.

ZA'A NEMI

1. Dabino mai kyau
2. Zuma

Da farko zaka jika dabinon a ruwa mai kyau bayan yayi laushi sai ka bare ka cire kwallayen sa,sannan kayi bleeding din sa kasa ruwa kadan bayan haka sai ka zuba zuma a ciki amma kar yayi ruwa ana so yayi kauri.
Sai ka ajeye kavrika shan shina chokali 3 sau 3 a rana,na tsawon wani lokaci, insha Allah zaka  samu waraka.daka dukkan masu cutuka da ka kamu dasu ta hayar istinba'i

Share this


Author: verified_user

0 Comments: