Sunday, 23 June 2019
Labari daga bangaren Fatima ta bakin yayan ta Hilal Dalhatu:

Home Labari daga bangaren Fatima ta bakin yayan ta Hilal Dalhatu:
Ku Tura A Social Media


"Wannan yarinyar kanwa tace, wallahi mutumin nan azzalumi ne. Kuma self defense tajeyi har tayi stabbing dinsa. Yanda ma akayi ta samu wukar dukanta yakeyi kamar zai kasheta ta samu ta kwace ta shiga kitchen, amma ya karya kofar kitchen din ya shigo yaci gaba da dukanta yana taka mata ciki, bayan yasan tana da juna biyu. Shine kawai ta rarimi wuka ta danna masa, a hakan saida ya zare wukar ya caccaka mata akanta da jikinta ds kuma gabanta. Allah yabi mata hakkinta.

"Amma mutane basu san gaskiyar abu ba su yita zagin yarinya. Kuma duk irin wannan abun da laifin iyaye a ciki. Mutum yana dukan yarinya tazo ta fada a gida amma an rufeta da fada cewa itace bata masa biyayya ko kuma ace wai tayi hakuri toya zatayi saboda Allah? Wannan abun ya faru yafi sau biyar yana dukanta, amma ta kasa zuwa ta fada. Saboda na farko daya farayi ta fada a gida cewa akayi laifinta ne aka hauta da fada. Shi yasa ya samu kofar cin karansa ba babbaka. Iyaye muji tsoron Allah akan 'ya'yayenmu."

Share this


Author: verified_user

0 Comments: