Thursday, 13 June 2019
Kunaji Fa Gwgwaggwon Biri Ake Zargi Da Sace Milyan Goma A Gidan Zoo Na Kano...

Home Kunaji Fa Gwgwaggwon Biri Ake Zargi Da Sace Milyan Goma A Gidan Zoo Na Kano...
Ku Tura A Social Media

Gidan Rediyon Freedon na Kano a daren nan, ya cigaba da bincike kan yadda aka yi naira miliyan goma cinikin da aka yi na Gidan Zoo na Kano a lokacin Sallah suka yi batan dabo.

Wasu jamiái sun ce suna zargin wani Gwaggwon biri da sace wadannan kudi, kuma ba a san inda ya boye ba.'. Sai dai suna zargin da ya sace hadiyewa ya yi.

Wakiliyar Gidan Rediyon Freedom da ta je Gidan Zoo yau da rana, ta samu dukkanin Ofisoshin manyan gidan a kulle, sai masu sayar da tikiti a bakin gate, da baki masu shigowa kallon dabbobi.

Amma wadansu ma'aikatan gidan Zoo, sun fada wa Wakiliyar ta Freedom cewa batun batan kudi a daina kalawa Biri, domin bai san komai ba a maganar, kuma ba shi da hannun a ciki, Suka ce akwai wadansu Birran masu siffar mutane da suka yi SIBARAN-NA-BAYYE da kudin. Suka ce ya za a yi birin ya balle kejinsa ya je ya sace kudi?

Wakiliyar Freedom ta ziyarci kejin da aka ajiye birin  da ake zargi da sace kudin, ýan kallo sun zagaye shi, suna kallonsa a matsayin barawo.

Shi kuwa Gwaggwon biri ya yi fakare, yunwar cikinsa ta ishe shi.

Sources: sarauniya.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: