Saturday, 22 June 2019
Ka Saurari Bangare Biyu Kafin Ka Yanke Hukunci (Ga mai bukatar gani video Da hoton yanzu)

Home Ka Saurari Bangare Biyu Kafin Ka Yanke Hukunci (Ga mai bukatar gani video Da hoton yanzu)
Ku Tura A Social MediaA yau na tashi da mummunan Labarin wata yarinya da su ka yi aure watanni bakwai kacal amma ta yanki mijinta wanda ke kwance a gadon asibiti , kasancewar ban fiye yadda da labaran social Media idan ba hujja na gani ba ya sa na saurara da yin fashin baki game da lamarin.

Cikin hukuncin Allah yanzu muka samu cikakken labarin na bangare biyu, rigima ce ta shiga tsakaninsu mijin ya hau matar da dukan tamkar zai kasheta wanda yanzu haka ya zubar mata da ciki na wata hudu, ganin yana shirin halaka ta kwaci kanta gurin rarumo wuka ta caka masa.
Bayan wannan hotunan akwai cikakken video na yadda jikin yarinyar ya munana da cuwuka, har da jinin da ta ke zubarwa na cikin da ya zube, da aka dauko daga police station din da aka kaita, har da cuwuka a cinya da kunne da kanta da targade Kala-Kala.

 Ga hotuna
Magana ta gaskiya dole iyaye mu mayar da hankali gurin tarbiyyar yaranmu da tsaurara bincike ga wanda za su aura, sannan bayan auran mu yawaita bibiyar zamansu, su matan kishi na rufe musu ido su yi ta bibiyar mazajan da bin kwaf da binciken wayoyinsu, yayin da mazan sun saba da shan shagali da Yan matan titi da ba za su iya dainawa ba ta wayoyinsu, sannan ga masifar shaye-shayen nan da ta addabi al'umma musamman matasanmu da su kan yanke kowanne hukunci idan sun bugu. Allah ya shiryemu baki daya.

Ga Bidiyo
Share this


Author: verified_user

0 Comments: