Saturday, 1 June 2019
Ina maka Nasiha Ne ko za kaji ,Ka Gaggauta Sakin Dasuki,Da El-zakzaky - Sheikh Ahmed Gumi

Home Ina maka Nasiha Ne ko za kaji ,Ka Gaggauta Sakin Dasuki,Da El-zakzaky - Sheikh Ahmed Gumi
Ku Tura A Social Media


Shahararren malamin nan na addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi yayi kira ga gwamnatin tarayya da ta saki tsohon mai ba kasa shawara a harkar tsaro a mulkin Goodluck Jonathan, Kanal Sambo Dasuki daga gidan yari.

Malamin Musuluncin ya kuma yi kira ga a saki Shugaban kungiyar yan uwa Musulmai na Shi’a, Sheikh Ibrahim Zakzaky.

Sheikh Gumi wanda yayi rokon a yayin rufe Tafsirinsa na wannan shekarar a masallacin Sultan Bello a ranar Lahadi yace gwamnati na bukatar bin umurnin kotu domin sakin mutanen biyu daga inda suke a tsare.

Gumi ya kuma ce babu wani fa’ida a ci gaba da tsare su tunda dai kotu tayi umurni kan a sake su.

Yace ya kamata gwamnatin tarayya ta yi zaman sulhu tare da Sheikh Zakzaky maimakon tsare shi. “Anan Najeriya, zan so gwamnati tayi duba ga lamarin Kanal Sambo Dasuki sannan ta sake shi ba tare da bata lokaci ba. Sannan su kuma saki Shugaban Shi’a, Sheikh Ibrahim Zakzaky

Share this


Author: verified_user

0 Comments: