Thursday, 27 June 2019
Ilmantar Da 'Ya'yan Jihar Kano Ya Fiye Min Dukkan Kadarorin Da Na Mallaka, Cewar Kwankwaso

Home Ilmantar Da 'Ya'yan Jihar Kano Ya Fiye Min Dukkan Kadarorin Da Na Mallaka, Cewar Kwankwaso
Ku Tura A Social Media


...don haka na saka kadarorina kasuwa a domin ilmantar da matasa a gida da wajen Nijeriya, cewarsa

Tsohon Sanatan Kano ta Tsakiya, Injiniya Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa zuwa yanzu ya saka kadarorin da ya mallaka a kasuwa domin ya nemi kudin da zai tura matasa karatu a makarantar gida Nijeriya da ma kasashen waje.

Tsohon gwamnan jihar Kano, Dr Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana haka ne a wata hira da yayi tare da gidajen rediyo a jihar Kano.

Majiyarmu ta DABO FM ta binciko cewa, Injiniya Kwankwaso ya bayyana cewa akwai filayen da aka ba shi musamman a jihar Sokoto wanda yace tsohon gwamnan jihar Sanata Aliyu Wammako ya bashi.

“Na saka filayen da na mallaka a kasuwa, domin neman kudin da za mu biyawa yaran da mukes on turawa karo karatu a makarantun gida da kasashen waje.”

“Ilmantar da ‘yan jihar Kano ya fiye min dukkanin kadarorin da na mallaka.”

“Fili na da yake Sokoto, an saida shi miliyan 35, yanzu haka kudaden suna nan a banki.”

Kwankwaso ya ce akwai filayen shi dake jihohin Yobe, Adamawa, Kaduna da Abuja wadanda a halin yanzu duk suke kasuwa domin neman kudin da gidauniyar za ta yi amfani da shi wajen biyawa daliban kudin makaranta.

Kwankwaso ya bayyana cewa gidauniyar Kwankwasiyya ta shirya tsaf domin daukar nauyin karatun dalibai 370 domin yin digiri na biyu a kasashen waje.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: