Monday, 24 June 2019
Gaskiyar Abinda Ya Faru Tsakanina Da Matata Hanan - Mijinta Sa'idu A Gadon Asibiti

Home Gaskiyar Abinda Ya Faru Tsakanina Da Matata Hanan - Mijinta Sa'idu A Gadon Asibiti
Ku Tura A Social Media

Daga  Imam A Saleh

Tun jiya lokacin da muka samu labarin faruwar wannan mummunan al’amari tsakanin wani magidanci Sa’idu Musa da ake zargin mai dakin sa Fatima Musa Hamza ta burma masa wuka watanni shida bayan daura auren su, munyi ta kokarin jin ta bakin Saidu kamar yadda mukaji daga bangaren Fatima wacce ake kira da Hanan, toh amma hakan bata samu ba duba da cewa yana kwance rai kwa-kwai mutu kwakwai a gadon asibitin Mallam Aminu Kano.

Idan ba’a manta ba dai Hanan tunda fari ta bayyana cewa mijin ta Saidu ya jima yana tsangwamar ta duk da cewar ta hakura ta zauna dashi bisa umarnin iyaye, amma hakan bai hana shi duka, da kyara da kuma cin mutuncin ta ba, tace hatta a lokacin da tsautsayin ya faru dukan ta yakeyi kamar yadda ya saba, bata san lokacin da ta wawuri wuka ta zurma masa ba cikin rashin sani, a wani kaulin nata kuma tayi hakan ne domin ta kare kanta.
Akwai kuma yan uwan ta da dama da sukai ta bayyana abinda suka sani dangane da wannan al'amari, ciki harda wanda yace matsalar ta samo asali ne run sa'adda Saidu ya shaidawa mai dakin sa cewa baya bukatar haihuwa, sai dai samun cikin da tayi bisa kuskure yasa ya shiga kyarar ta.
Toh sai dai kamar yadda dokar aikin jarida ta tanadi damar jin ta bakin kowanne bangare dangane da wani sha'ani irin wannan, mun samu ganin Saidu yau da misalin marfe 11 saura a gadon sa na asibiti bayan farfadowar daga nisan zangon da yayi sakamakon wannan al’amari da ya auku a kansa.

Da fari na soma yi masa tambaya ne akan ko me zaice dangane da wannan al’amari da ya faru a kanshi ?, sai ya kada baki yace eh toh shi a ganin sa kawai mukaddari ne daga Allah, kuma ba shakka shi yana son matar sa (Hanan), sai dai tun kafin suyi aure ita a nata bangaren bata son shi, mahaifiyar ta sai ta matsa aka sake dawo da maganar don shi da yaga haka ma har ya rabu da ita, toh daga baya dai akazo akayi aure bisa tunanin ko Allah zaisa daga baya ta dawo tana son shi.
Sai dai bayan aure sabanin haka ce ta rika aukuwa, domin cikin watanni shiddan nan babu wani cigaba da aka samu hasalima a koda yaushe sa’in sa kawai suke samu a tsakanin su.
Saidu ya cigaba da shaida min cewa kaga dai ni ba ma a garin nan nake zaune ba a Gusau (Zamfara) nake aiki na, sai na dan samu sarari haka sai in dawo hutu gida wajen mata ta, amma daga baya sai na samu cikakken bayani daga majiya mai tushe na cewa ita mata ta (Hanan) tana kawo maza idan bana nan, daga bisani sai kuma na gano cewa ta hada baki da wasu masu gadi na su biyu wadanda su suke boye min wannan al’amari a duk sa’adda nayi kokarin tabbatar da zargin da nakeyi.

A lokacin da na tabbatar da wannan al’amari sai na kori wadannan masu gadi biyu da take hada baki dasu na bar mata daya, na kwace wayoyin ta na kuma gargade ta sosai akan wannan dabi’a tata, sai dai hakan baisa ta daina ba, inji Sa'idu.

Haka nan muka cigaba da zama cikin wannan matsala domin ni nasawa raina aure cike yake da kalubale, toh amma ita a nata tunanin kawai na hana ta sakewa ne, rannan ina kwance karfe 12 na dare naji ana ta kawo min suka da wuka, ashe wai mata ta ce ta farmin da suka da wuka, a nan na kamata da kokawa domin inga na kwace wukar dake hannun ta amma tuni tayi nasarar zurma min a ciki har saida kayan ciki na suka zazzago, haka dai nayi ta kokawa da ita har saida ta sake yanka ta, a garin kokarin kwace wukar ne ta daki gefen gado ta kurje a jikin ta, a cewa Sa'idu.

Ganin na kwace wukar ne na ruga waje da gudu nasa mai gadi ya rufe gida karya barta ta fita, ni kuwa muka kama hanyar asibiti da makota wadanda suka suka rarrafa dani zuwa asibiti, haka muka dangana ni kuwa na toshe kayan ciki na da suka zazzago da hannu, inji Sa’idu.

Na sake tambayar Mallam Saidu “””Toh amma ai tace kana dukan ta hasalima a garim kokarin kare kanta wannan al'amari ya auku, ””””, sai yace wannan ta fada ne kawai watakila saboda ta kare abinda tayi, amma dai ina son in tabbatar maka da cewa ban taba dukan mata ta ba kuma kamar yadda na gaya maka tunda farko ni fa nake son ta ita bata so na, kuma hasali ma ina da kyamarar nadar bayanan sirri ta CCTV a gidan tana daukar kumai, za'a iya dubawa a gani, kamar yadda Sa'idu Musa, mijin Hanan ya bayyana a zantawar mu dashi.

Bayan ya gama min wannan bayani ne ya koma ya kwanta, kafin daga bisani muka dauki wannan hoto nashi mukayi sallama.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: