Saturday, 29 June 2019
Fim Din SAREENA Ya Kafa Sabon Tarihi A Kannywood

Home Fim Din SAREENA Ya Kafa Sabon Tarihi A Kannywood
Ku Tura A Social Media

A rananr Juma'ar nan da ta gabata masana'antar Kannywood ta kara samun tagomashi sakamakon sabon tarihi da fim din SAREENA ya kafa yayin da ake nuna shi a Sinima.

Fim din, wanda kamfanin Maishadda Investment suka shirya tare da gabatarwa, ya hada jarumai irin su Ali Nuhu, Umar M Shareef, Shamsu Dan Iya, Maryam Yahaya da sauran su.

SAREENA ya zamo fim na farko da ya mamaye dukkanin sinimun Ado Bayero Mall, sakamakon yadda 'yan kallo suka cika wurin tare da saye tikikitansa gaba daya.

Kasancewar Umar M Shareef da Maryam Yahaya sun fito a matsayin makafi, hakan ya sa fim din ya samu karbuwa a wurin 'yan kallo.

Yanzu haka labarai sun tabbata cewar kamfanin Mai Shadda na samun makudan kudade ta dalilin wannan fim.

Northflix za ta dora fim din SAREENA a Manhajarta ranar Litinin domin wadanda suke nesa su samu damar kalla.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: