Thursday, 27 June 2019
Fama da Jin Zafi Yayi Jima'i Saduwa (painful intercourse)

Home Fama da Jin Zafi Yayi Jima'i Saduwa (painful intercourse)
Ku Tura A Social Media
Jin zafi yayin saduwa ababe daban daban Kän jawo hakan kama da zafi daga waje-waje farko farkon da azzakarin maigidan ya fara shiga jikin macen.
JIN ZAFI A FARKO-
Shine fara jin tun kafin mutum ya gama ratsa farjin mace sosai ya kai ga deep penetrating.
Abunda Kän jawo irin wannan zafin akwai;
1- Rashin ni'ima ko ruwan farko farko mai yauki dakan fara fitowa yayin da sha'awa ta fara motsowa sosai. Abunda Kän jawo rashin lubrication din bai wuce rashin fara wasanni wato foreplay kafin fara saduwa.
2- Raguwar sinadarin oestrogen ajika ga macen dake gab da daina haila, Rashin jimawa da haihuwa ko shayarwa.
3-Akwai kuma nau'in magunguna da suma Kän kai ga dauke damshi a farjin mace wanda hakan kansa jin zafin irinsu magungunan (hawan jini, nasa bacci, na farfadiya, magungunan kawar da damuwa, na allergies/mura, dana bada tazarar haihuwa.
4- Jin rauni a farji Sakamakon tura yatsa ciki ya zamto farcen mutum ya haifar da rauni, ko wani abun daban kamar faruwar hatsari, operation na kugu.

5- Kaciyar mata da akanyi nan ma ga macen da akama irin wannan Kän fuskanci zafin, ko Qari da akanyi ma mata yayin haihuwa, ko shigar kwayoyin cuta Kän fatar farji, da sauran nau'in cuttukan fata daka iya shafar farji.
7- Ko mace ya zamto mai tsukakken gaba yayin penetrating zata iya fuskantar zafi.
SAI KUMA ABABE DAKE SA JIN ZAFI DAGA CIKI
Wato zafi yada deep penetration. Wannan Mafi yawa Kän faru ne Sakamakon wasu cuttuka kamar;
1)- Cuttukan mara,
2)- Qarin cikin mahaifa (fibroid),
3)- Zazzagowar mahaifa (uterine prolapse),
4)- Canjin halittun cikin mahaifar mace,
5)- Ciwon mafitsara,
6)- Cutar basir,
7)- Karancin majinar cikin hanji dake tafiyar da abunda ke ciki,
8)- Taruwar ruwa a kwan halitta (ovarian cyst),
9)- Shigar kayan aikin likita jikin mace yayin maganin Ciwon jeji wato radiotherapy and chemotherapy.

SAI KUMA DALILI MAI ALAKA DA AIKIN KWAKWALWA
A- FUSHI; wato kila sanda maigidan yazo ita matar dama bataso wannan kanyi tasiri.
B- Damuwa ya zamto akwai wani Abu rai ba abama saduwar cikakken attention ba.
C- Yanayin yadda mutum ya bayyana ga macen wani yakan tsorata
D- Ko ya zamto dama ba wata jituwa tsakaninku yanxu da taka ta taso kazo kana lallashinta wannan kanyi tasiri gareta.
E- Idan ka zamto mai tumbi wato kugunka bai zamto flat ba
F- Idan ya zamto antaba cin zarafin mace wato kamar fyade ds.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: