Tuesday, 18 June 2019
Da Allah Ganduje Yake Fada, Daurawa Ya Yiwa Ganduje Shagube

Home Da Allah Ganduje Yake Fada, Daurawa Ya Yiwa Ganduje Shagube
Ku Tura A Social Media

Allah Ne Ya Yi Kano A Haka Kuma Yake So Ya Ganta, Shi Ya Sa Ya Albarkace Ta Da Abubuwa Guda shida:

1. Ilimin addinin Musulunci da malamai; Kano tafi ko wacce jiha yawan Malaman Addinin musulunci, shi yasa zaka ga mafi yawan mashahuran Malamai daga dariku da kungiyoyi na Addinin musulunci a Nigeria ko dai 'yan Kano ne, ko a Kano suka yi karatu ko Kuma suna zaune a Kano ko suna da Gida a Kano. Wannan ne yasa, Kano ta Zama cibiyar Addinin Musulunci na a Africa.

2. Sarauta da Sarakuna masu daraja; Masarautar Kano bata da na daya a Nijeriya duba da girma da kwarjini da Kuma tumbatsa da Allah ya yi Mata a Nijeriya.

3. Kasuwanci da manyan mashahura 'yan Kasuwa misali, Dantata, Dangote, Abdussamad da sauransu da yawa. Kasuwanni: Kasuwar kwari, Kurmi, Sabon Gari, Dawanau, Kofar Wambai da sauran su.

4. Siyasa da manyan 'yan Siyasa duk Nigeria Babu Jiha da take da manyan 'yan Siyasa kamar Kano, Siyasar Kano ta Sha bambam da sauran Jihohi kamar yadda Marigayi Malam Aminu Kano ya Dora ta. Muna da mashahuran 'yan Siyasa da babu wata Jiha da take da irinsu a tarihi da bazan Kama suna ba Saboda wasu dalilai.

5. Allah ya albarkaci Kano da 'yan takarda masu dimbin yawa, wato 'yan Boko da Kuma manyan makarantu.

6. Na Karshe shine yawan Al'umma, ko Kuma 'yan Dangwale, Wanda muka Kasa su kaso biyu, wato Baki da 'yan Gari.

Dukkanin wadannan abubuwa Allah ne ya albarkaci Kano dasu. Binciken mu ya nuna cewa akwai wadanda suka dakko kwangilar Rusa Kano ta yadda zasu Rusa Arewa, Saboda idan ka Rusa Kano to kamar ka Rusa Arewa ne, Saboda duk abinda yayi tasiri a Kano to tabbas zaka ga ya shafi Arewa.

Wadannan marasa kishi an hada Kai dasu ana Bata sunan Yan Arewa da lalata mu'amular yan Arewa da Siyasar Kano Domin biyan bukatar abokan Zaman mu na Kudu, musamman a kakar Zabe Mai zuwa.

Saboda Haka muke sanar da wadannan Mutane cewa duk makirce-makaircen su, duk sharrance -sharrancen su ga Kano bazai tasiri ba Saboda Kano Allah ne yayi ta Haka Kuma Yake so ya ganta a Haka Saboda Haka FADA DA KANO KAMAR FADA DA YIN ALLAH NE.

Muna rokon Allah duk Wanda Yake nufin Kano da Arewa da wani mugun nufi Allah ka shirye shi in Kuma bazai shiryu ba Allah kayi Mana maganinsu, Allah ka bawa Nigeria Zaman lafiya da cigaba Mai dorewa...

®Hausadailypost

Share this


Author: verified_user

0 Comments: