Sunday, 23 June 2019
Ana kishin-kishin cewa Buhari zai bawa tsohon kwamishina 'yan sanda 'Singham' rikon wata hukuma

Home Ana kishin-kishin cewa Buhari zai bawa tsohon kwamishina 'yan sanda 'Singham' rikon wata hukuma
Ku Tura A Social Media
Wani labari da ke yawo a kafafen yada labarai da sada zumunta na nuni da cewa wata majiya mai karfi da ke da kusanci da fadar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta bayyana cewa shugaba Buhari na shirin bawa tsohon kwamishin 'yan sanda a jihar Katsina da Kano, CP Muhammad Wakili, mukami.

Tsohon kwamishina Wakili da aka fi sani da 'Singham' ya bar aiki ne a cikin watan Mayu.

Singham ta shiga bakin jama'a ne bayan kwamishinan ya yi tsaiwar gwamen jaki wajen hana rikicin daba da bangar siyasa lokacin yakin neman zaben 2019.

Majiyar fadar shugaban kasa ta ce mai yiwuwa shugaba Buhari ya bawa Singhanm rikon hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA).

A cewar Majiyar, shugaba Buhari ya yaba da aikin Singham lokacin da ya ke rike da mukamin kwamishinan 'yan sanda a jihar Katsina da Kano.


"Ina mai shaida maka cewa maigida (Buhari) ya kalli bidiyon nan na CP Wakili wanda yake magana a kan yadda manya da yara, maza da mata, ke shan miyagun kwayoyi, kuma ya yaba da aniyarsa ta yaki da shaye-shaye," a cewar majiyar, kamar yadda Hantsi24 ta wallafa.

Majiyar ta bayyana cewa ba abin mamaki ba ne a tsinci sunan CP Wakili a cikin sunayen mutanen da shugaba Buhari zai bawa mukami a zangon gwamnatinsa na biyu.

®Legit

Share this


Author: verified_user

0 Comments: