Saturday, 1 June 2019
An Yi Mini Tayin Miliyan 30 Domin Kare Ganduje – Sheikh Abduljabbar Kabara

Home An Yi Mini Tayin Miliyan 30 Domin Kare Ganduje – Sheikh Abduljabbar Kabara
Ku Tura A Social Media


Sheikh Abdujabbar Nasiru Kabara yace duk wani malami da yake fitowa ya hau manbari wajen kare Mai girma gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Ganduje, akan bidiyon da akaga gwamnan yana karbar cin hancin daloli, biyanshi akayi makudan kudade


“Duk wani malami da kukaji yana cewa ayi jami’iyyar APC a Kano, Kudi aka bashi. Ina da yakini shiyasa yanzu naga dole in musu nasiha.”
Yayi kira ga malamai da su kasance masu duba masalahar al’umma wajen goyon bayan gaskiya a koda yaushe.

“Ina jan hankalin malamai, su dubi Allah suji tsoransa, su kiyayi siyasantar da addini. Nima ba tayi ne ba’ayi min ba, na auna ne naga bazanyi ba, kuma ina fada duk kudi aka basu.”
Sheikh Kabara ya kara bayyana yadda wasu makusantar gwamnatin jihar Kano suka iske shi , tare da yi masa tayin fitowa ya karyata maganar faifan bidiyon da Jaridar Daily Nigerian ta fitar, wanda akaga gwamna Ganduje yana sunkume kudi samfurin dakar Amurka a aljihun babbar rigarshi.

“Ana nan sai ga wasu jakadu sun kuma zuwa da naira miliyan 30 a hannu da kuma sabon tayi. Suka ce babu rufe-rufe, akan faifan bidiyo ne, so ake ka fito kace karyane.”

Malamin ya nesanta kanshi ga masu cewa yana tarayya ko kuma goyon bayan sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Daga karshe yayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da kada ya zura ido
“ina kira ga Baba Buhari, ka duba Allah, duk wanda yaci zabe a bashi zabenshi, wanda ya fadi, duk wata tashin-tashina a dauko ta a jingine. Wannan shine abinda yakamata kayi ba zura ido anata shirin tada hargitsti ba.”

Source: Muryayanci.com

Share this


Author: verified_user

0 Comments: