Saturday, 22 June 2019
Amarya a Kano ta caccakawa mijinta wuka bayan aurensu da watanni 6

Home Amarya a Kano ta caccakawa mijinta wuka bayan aurensu da watanni 6
Ku Tura A Social Media
Amaryar dake zama a jihar Kano ta caccakawa mijinta wuka a ciki bayan zamansu na watanni 6.

Matar mai suna Fatima Musa ta caccakawa mijinta mai suna Sa’eed Muhammad Hussain wukar a cikinshi mai dauke da guba, kamar yadda majiyoyi suka tabbatar.Bisa bincike, DABO FM ta gano yanzu haka Sa’eed Muhammad yana kwance a asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano inda yake karbar kulawa daga wajen likitoci a yanayin yanzu.


A nasu bangaren, yan uwan Fatima Musa sun hallara a asibitin Mallam Aminu Kano inda suka bayyana cewa “Yar su bazata taba aikata wannan mummunan aiki ba.”

Sai dai DABO FM ta binciko cewa wannan ne karo na 3 da Fatima Musa tayi yunkurin hallaka mijinnata a kasa da watanni 6 na aurensu.Majiyoyin dai sun tabbatar da an taba kama Fatima Musa da niyyar halaka Sa’eed da zuba masa guba.

Masu Alaƙa  Kano: Budurwa 'yar shekara 17 ta kashe kanta saboda mahaifinta ya saki mahaifiyar ta
Sai dai an tabbatar da Fatima Musa tana shan kwayoyi masu gusar da hankali tin lokacin da take ‘yan matanci inda kuma aka bayyana cewa ba auren dole akayiwa Fatima ba.

Sai dai a tabbatar da babu wata cikakkiyar soyayya mai karfi dake tsakaninsu.

Yanzu haka dai Fatima tana tsare a hannun rundunar ‘yan sandan jihar Kano.

Tin bayan rikicin Maryam Sanda, amaryar shekara 1 da ake zargi da caccakawa mijinta wuka, al’amarin yunkurin kisa ga mazaje daga matansu ya zama ruwan dare a arewancin Najeriya.

Daga nan anyi ta samun matsaloli tsakanin ma’aurata wanda matan suke daukar hukuncin hallaka miji.

A Kaduna an samu labarin matar data shararawa mijinta ruwan zafi.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: