Monday, 3 June 2019
Ali Nuhu ya bude kantin saida tufafin 'yan gayu a Kano

Home Ali Nuhu ya bude kantin saida tufafin 'yan gayu a Kano
Ku Tura A Social Media
Ali Nuhu Ya Raba Kafa

Ali Nuhu ya bude kantin saida tufafin 'yan gayu a Kano shekaranjiya.

Kantin, mai suna Don Ali Collection, an bude shi ne a shago na 10 a gidan kantina mai suna Nation Plaza wanda ke lamba 9, Titin Audu Bako, a Kano.

Manyan 'yan fim irin su Sani Danja, Yakubu Muhammad, Nazifi Asnanic da Ramadan Booth da kuma fitattun 'yan kwallo din nan da ke bugawa a kasar waje, wato Ahmed Musa da Shehu Abdullahi, sun halarta.

A shekarun baya, Yakubu Muhammad ya taba bude irin wannan shagon.

Mujallar Fim ta fahimci cewa wannan abu da Ali ya yi, yunkuri ne na fadada hanyoyin sa na samun kudi ta harkar kasuwanci, abin da bai saba yi ba. An jima ana ba shi shawarar cewa ya hada harkar fim din sa da kasuwanci don cin tudu biyu.

'Yan fim da dama su na yin harkokin kasuwanci. Akwai masu saida motoci, bada gidaje haya, shagon gyaran gashi, sayar da tufafi, man shafawa, turare,  ogogo, takalma, saida fim, saida waya, sufuri, kwangila, aikin gona da sauran su.

Ali Nuhu da Adam A. Zango na daga cikin kalilan da su ka dogara kacokam da harkar fim saboda yadda su ke damawa a cikin ta.

Tuni dai samun kudi ya yi rauni a harkar, don haka tilas ne 'yan fim su raba kafa domin fadada hanyoyin su na samun kwabo.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: