Thursday, 2 May 2019
Ronaldo ya sayi mota mafi Tsada a Duniya

Home Ronaldo ya sayi mota mafi Tsada a Duniya
Ku Tura A Social Media

Dan wasan Juventus Cristiano Ronaldo ya kafa tarihin sayen mota mafi tsada a duniya.
Ronaldo ya sayi motar kirar Bugatti, mai suna “La Voiture Noire” wato bakar mota a hausance, kan kudi Euro miliyan 11, wato kwatancin Naira Biliyan 4 da miliyan 448, da dubu 883, da dari 862.

Wannan mota da Cristiano ya saya dai, irinta guda daya kawai kamfanin motocin na Bugatti ya kera a halin yanzu, a wani bangare na bikin cikarsa shekaru 110 da kafuwa.

To sai dai wanda ya mallaki wannan mota, wato Cristiano, ba zai tuka ta ba, har sai shekarar 2021, saboda uzurin cewa akwai sauran nazarin kamfanin na Bugatti ke karasawa akanta.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: