Sunday, 19 May 2019
Manufar Taron Yan Kannywood Dasunkayi Akan Northflixng A Jiya Kano (Karanta)

Home Manufar Taron Yan Kannywood Dasunkayi Akan Northflixng A Jiya Kano (Karanta)
Ku Tura A Social Media
Majiyarmu hasaloaded ta samu wannan ne daga shafin babban darakta falalu dorayi ga  jawabinsa.


NorthFlixng tana mika godiya ga duk masu ruwa da tsaki da suka sami halattar bikin kaddamar da manhajar a tallata finafinai a yanar gizo,

Wannan wata dama ga ma’abota kallon finafinai wadda zata yi daidai da raayinku a zamanance. Daga yanzu daga konina kake a duniya kana iya kallon kayatattun finafinai masu gajere da dogon zango a kan manhajar yanar gizo ta www.northflixng ko ta Manhajar Northflixng da ke dandalin playstore da AppStore.

Manhajar ta saukaka muku wajen neman fayafayan CD ko DVD ku na kwance a kan gadonku za ku sha kallo ku more ta amfani da wayar salula, ko laptop, ko tablet ko kuma Smart tv.

Garabasar manhajar Northflixng ba ta tsaya kan 'yan kallo ba kawai,  ina masu shirya finafinan Hausa, lokaci yayi da za ku fara shirya kayatattun finafinai wadanda za ku sayar da su kai tsaye ga masu kallo a ko ina a duniya a kan manhajar Northflixng

Hankali kwance kana daga daki za ka ji makudan kudi na shigo ma ba kakkautawa kuma babu ranar yankewa.

Marhabun da zuwan manhajar Northflixng wacce za ta fara aiki nan da wani lokaci ba mai tsayi ba. Bisa jajircewar haziki kuma Jagora @jamil_hajaj

Northflixng tana maraba da duk wani fim ingantacce mai ma'ana, wanda yai dai dai da tsarin manhajar.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: