Saturday, 18 May 2019
Kiris ya hana in auri Nafisa Abdullahi da Fati Washa - Inji Adam A. Zango

Home Kiris ya hana in auri Nafisa Abdullahi da Fati Washa - Inji Adam A. Zango
Ku Tura A Social Media


A wata hira da yayi da BBC, tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki,Adam A. Zango ya bayyana yanda yayi soyayya da abokan aikinshi, Nafisa Abdullahi da kuma Fati Washa wadda har ta kusa kaiwa ga Aure amma Allah be yi ba.
Adam ya bayyana cewa yayi soyayya da Nafisa Abdullahi a kusan shekaru 3 da suka gabata amma daga baya suka rabu, wannan be hana sun ci gaba da sanarsu ba da kuma girmama juna.

Yace irin wannan na faruwa a ko'ina, mutum yayi soyayya da budurwa wani dalili yasa su rabu ya kuma koma yana yi da wata.
Ya kara da cewa itama Fati Washa sun yi soyayya sosai har kadan ya rage su yi aure amma Allah be yi ba.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: