Kannywood

Iyayena Sun Sa Albarka A Shigata Harkar Fim —Jaruma Hadiza Muhammad

Tattaunawar WAKILINMU, MUSA ISHAK Muhammad Tare Da JARUMA HADIZA MUHAMMAD Ta Masana’antar Kannywood.
Za Mu So Mu San Takaitaccen Tarihin Jaruma Hadiza Muhammad.
Salamu alaikum, sunana Hadiza Muhammad kuma a kan yi min inkiya da Hadizan Saima. Ni ‘yar Kano ce, an haife ni a Fagge amma na girma a unguwar Brigade, na yi karatun firamare da sakandire wanda daga nan ne kuma nayi aure har Allah ya albarkace ni da samun ‘ya‘ya biyu. Daga baya ne kuma bayan mun rabu da mijina sai Allah ya sa na tsinci kaina a masana’antar fim.
Shin Kina Da Alaka Ta Jini Ne Da Jaruma Saima, in aka lura da Lakabin Da Ake Miki Da Hadizan Saima?

Lallai ina da alaka ta jini da Saima mana tunda Musulma ce kuma nima musulma ce, amma dai dangantakar mu shi ne mu kawaye ne, kuma Allah ya zo ya hada mu a masana’anta daya, amma ba ‘yan uwa bane na jini kamar yadda mutane suke cewa ya da kanwa ne. Kuma ita ta riga ni shigowa wannan masana’anta, hasali ma ita ce ta zamar min tsani na shigowa wannan masana’antar, domin ita ta ringa hada ni da abokan aiki har aka san ni aka fara aiki tare da ni.
A Matsayinki Na Mace, Wane Irin Kalubale Kika Samu Musamman Daga Gurun Iyaye Da ‘Yan Uwa A Lokacin Da Kika Shiga Harkar Fim?
Gaskiya ni ban fuskanci wani kalubale ba, saboda kusan na shigo wannan masana’anta ne da girmata ba wai yarinya ‘yar karama ba kamar yadda wasu suke shigowa a yanzu, tunda har na yi aure na haihu kafin na shigo. Kawai da naga harkar fim akwai abubuwa da dama da suka ja hankalina wanda nake ganin nima zan iya bada gudunmawata. Sannan abu na biyu kuma sana’a ce. Iyayena kullum saka min albarka suke. Suna yi min addu’a idan zan fita, kuma suna min sannu da zuwa idan na dawo daga aiki.
A Lokacin Da Kika Shigo Wannan Masana’anta Ta Finafinai Wanne Ne Fim Dinki Na Farko Da Kika Fara Yi?

Fim dina na farko, akwai wani fim da muka yi mai suna “Sakar Zuciya” amma fim din na ‘yan kungiya ne a lokacin ana kungiyoyi na dirama, to a wannan lokacin su ‘yan kungiyar su suka hada wannan fim din, shi ne dai kusan fim dina na farko wadda aka fara saka min na’urar hoto (camera).

Wannan Fim Na Sakar Zuciya Kina Ganin Kamar Shi Ne Silar Haskawarki A Duniya Ko Kuma Akwai Wani Fim Wanda Shi Ne Ya Zama Silar Haskawar Jaruma Hadiza Muhammad?
To kusan wannan fim na Sakar Zuciya ma shi bai fita kasuwa ba, iyakacinsa gidajen sinima domin a lokacin ana amfani da sinima ne, amma dai ina fadar sa ne saboda shi ne kusan farko. Amma bayan shi gaskiya akwai finafinai da yawa wanda suka fita kusan lokaci daya, wanda zan iya cewa su ne suka zama silar da aka sanni sosai. Amma bazan iya kama sunan wani fim guda daya ba in ce shi ne ya zama silar haskawa ta, saboda finafinan suna da yawa kamar yadda na fada.
Zuwa Yanzu Kin Samu Kamar Shekaru Nawa A Cikin Wannan Masana’anta Ta Finafinai?
Zuwa yanzu na samu kusan shekara goma sha shida 16 zuwa goma sha bakwai 17 a cikin wannan masana’anta.
Duba Da Irin Wannan Shekaru Da Kika Dauka A Cikin Wannan Masana’anta, zuwa Yanzu Kin Fara Yin Fim Mallakinki Ne Ko Dai Har Yanzu Kina Fitowa Ne A Matsayin Jaruma?

Gaskiya nayi a baya amma na hadin gwiwa ne, amma inshaAllah nan da dan lokaci kadan zan fara yin nawa na kaina, mallakina ba tare da hadin gwiwar wasu ba.
Ya Ya Za Ki Bayyana Alakarki Da Daraktoci, Furodusoshi Da Kuma Sauran Jarumai Abokan Aiki?
Alhamdulillah, Muna mu’amala ta arziki, muna mutunta juna, komai kankantar mutum in yazo a kan aikinsa ina mutunta shi nima ana mutunta ni. Saboda haka a iya sani na har zuwa yandu ba ko mutum daya da zai ce ina da wani sabani da shi, daga daraktocin da furodusoshin da kuma jaruman. Muna rayuwa ta mutunta juna, kuma muna aiki cikin farin ciki muna yi wa juna san barka.
Wacce Shawara Zaki Bawa Mata Masu Sha’awar Shiga Sana’ar Fim?

To har kullum dai, kamar mu da muka dauki fim a matsayin sana’a gaskiya muna martaba fim, kuma muna kokarin mu ga mun kare mutuncinmu da na addininmu da na al’adarmu. Sabanin wasu yara kanana da suke kallon kyale-kyale na fim suke so su shigo don cinma wata manufa. Bance duka ba, amma wasu daga ciki, wanda suna daya daga cikin wanda suke zuwa su dagula mana masana’antar nan. Su suke jawo mana zagi, sai mace daya ta je ta aikata wani laifi, amma sai a yi mana kudin goro a zage mu gaba daya, a yi mana mummunar fahimta. A sakamakon haka yanzu hukumomi sun tashi tsaye domin tace duk wata wadda take shirin shigowa wannan sana’a. An shigo da tsari na sai an samu amincewa daga gidanku, mai unguwarku ya saka miki hannu, sannan za a baki shaidar shigowa wannan masana’anta, sannan a fara saka ki a cikin fim.
Me Ce Ce Shawararki Ga ‘Yan Uwanki Jarumai Wajen Kula Da Mutuncinsu Da Kuma Mutunta Sana’arsu, Duba Da Irin Rikicin Da Ya Barke A Kwanakin Nan A Tsakanin Jaruma Hadiza Gabon Da Jaruma Amina Amal?

To kusan ba masana’antarmu kadai ake samun rikice-rikice ba, kamar yadda na fada kusan duk duniya indai mutane za su hadu to za a iya samun rikici ko zaman lafiya. To wannan wani abu ne da ya shafe su kusan mu bai shafe mu ba. Wani rikici ne da za su iya zama su sulhunta kansu. Kuma zuwa yanzu an tsawatar musu iya tsawatarwa, yadda wani ma zai ji shakka ko tsoron aikata wani abu irin wannan.
Me Ne Ne Sakonki Ga Masoyanki Masu Jin Dadin Kallon Finafinanki?

To masoyanmu dai har kullum muna gode musu kuma muna musu fatan alkhairi kamar yadda suke mana. Wadanda muka sani da wadanda muke waya da wanda ma ba za mu ga juna ba har abada, muna musu fatan alkhairi mun gode da kaunar da suke nuna mana, kuma Allah ya bar zumunci a tsakaninmu. Muna roko da su ci gaba da yi mana addu’a, kuma duk inda suka ga mun yi kuskure to su sanar da mu, domin babu wani dan Adam da baya kuskure, kuma a shirye muke da mu karbi gyara, mun gode sosai.
Mun Gode Kwarai Da Gaske
Nima na gode

Sources: Leadershipayau.com

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? ?‍?
? Hi, how can I help?