Tuesday, 21 May 2019
Fitattun Taurarin Kannywood 6 Da Har Yanzu Basu Shiga Daga Ciki Ba

Home Fitattun Taurarin Kannywood 6 Da Har Yanzu Basu Shiga Daga Ciki Ba
Ku Tura A Social MediaMasana’antar fina finan Hausa da aka fi sani da suna Kannywood a cike take da mashahuran yan wasa, musamman ma jarumai Mata, wadanda suka kai bantensu a harkar iya wasan kwaikwayo musamman duba da yadda suke baje kolin kwarewarsu a fina finan Hausa.


Sai dai baya da shahara da kuma fice da wadannan jarumai Mata suka yi, karin riba a garesu shine Allah Yayi musu zubin kyau, kyawun jiki da kuma kyawun fuska, ta yadda duk wanda ya kallesu sai ya maimaita, amma kash! Ba dukansu suka samu mazajen aure ba.

Jaruman
Ya kamata mai karatu ya kwana da sanin cewa ba muyi wannan rahoto don cin fuska garesu ba, a’a, sai dai don sanar da duniya gaskiyar lamari a matsayinmu na masu bibiyan al’amuran taurarin fina finai, don haka muka kawo muku wasu daga cikin fitattun jarumai mata guda shida da suka yi suna a harkar Fim amma basu da mazaje, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito,
Ummi Zeezee
Jaruma uwar jarumai, watau Ummi Ibrahim mai inkiya da Zee Zee ta ciri tuta wajen taka muhimmiyar rawa a fina finan Hausa musamman a gomman shekaru da suka gabata, kasancewarta dadaddiya a Kannywood amma bata da aure, hakan bai sa kyawaunta ya bace ba.
Hadiza Gabon
Jaruma Hadiza Aliyu Gabon yar asalin kasar Gabon ce, wanda aka haifeta a ranar 1 ga watan Yuni na shekarar 1989 a babban birnin kasar Gabon, Libreville, ta fara samun shahara ne a Fim din Ali yaga Ali.
Tabbas Hadiza Gabon na daga cikin fitattun kyawawan yan mata dake taka rawar gani a masana’antar fina finan Hausa ta Kannywood.
Nafisa Abdullahi
A wata hira da Adam Zango yayi a makon data gabata ya bayyana yadda saura kiris maganan aurensa da Nafisa ya tabbata, amma Allah bai yi ba, jaruma Nafisa, baka, siririya kyakkyawa ta samu shahara ne a cikin Fim din ‘Sai wata Rana’, kuma a shekarar 1991 aka haifeta a garin Jos na jahar Filato.

Rahama Sadau
Tauraruwar Rahama Sadau ta kara haskaka tun bayan gwaramar data samu da hukumar tace fina finai ta jahar Kano biyo bayan wani bidiyon waka da tayi da mawaki Classiq, wanda hakan yasa shahararren mawaki Akon ya gayyaceta zuwa Amurka.
A watan Disamba na shekarar 1992 aka haifi Rahama a garin Kaduna, kuma tayi karatun digiri a fannin gudanar da kasuwanci daga wata jami’a dake kasar Cyprus.
Fati Washa
Fatima Abdullahi wanda aka fi sani da suna Fati Washa an haifetane a ranar 21 ga watan Feburairun shekarar 1993, kuma ta kasance guda daga cikin taurarin Kannywood da suka yi fice a aikinsu, daga cikin manyan fina finan data fito akwai Rariya.
Hafsat Idris
An haifi jaruma Hafsat Idris a garin Sagamu na jahar Ogun ne, amma yar asalin jahar Kano ce, Hafsat ta fara samun shahara a Kannywood ne a yayin da ta fito a fim din Barauniya, wanda shine Fim dinta na farko.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: