Tuesday, 21 May 2019
Dr Sheikh Isa Ali Pantami Ya Fadi Gaskiyar !!! Karanta Kaji...

Home Dr Sheikh Isa Ali Pantami Ya Fadi Gaskiyar !!! Karanta Kaji...
Ku Tura A Social Media


Shugabannin Najeriya Ba Addu'a Suke Bukata Ba Face Kawai Afadamusu Gaskiya, Shehun Malami Isah Ali Ibrahim Pantami Shine Yayi Wannan Maganar A Tafsir Dinsa Da Aka Saka A Daya Daga  Cikin Gidajen TV Dake Daukar Tafsirin Shi a jiya Litinin .

Shehun Malamin Yabayar Da Misalai Na Kasashen Dasukaci Gaba Irinsu, Saudia, Ingila Da Amurka Inda Yace Tabbatar Da Adalci Shine Jigo Na Cigaban Kasashen, Yace Karyane Kaje Saudia Kaji Ana Sauke Qur'ani Da Sunan Wai Ayiwa Shugabani Addu'a Suci Gaba Ko Ayi Sbd Samun Cigaban Kasa.

Yace, A Najeriya Ne Kawai Zakaga Ana Sauke Qur'ani Kamar Me Da Sunan Asamu Cigaba A Kasar, "Addu'a Ba Itace Maganin Matsalarmu Ba, Dan Da Itace To Da Tuni Duk Duniya Babu Kasar Da Za Takai Najeriya Cigaba Domin Akwai Jahar Da Ake Sauke Qur'ani Kusan Dubu 70 Wata Jahar Dubu 10 Wata Kuma Hutu Za'a Bayar Aduk Jahar Aje Ayi Addu'a Duk Da Sunan Asamu Cigaba A Kasa."

Yakara Da Fadin Cewa, Adalci Shine Babban Abinda Za'a Rike Na Ganin Ansamu Ancigaba, "A Fadawa Shugabanni Gaskiya Bawai Aje Amusu Addu'ar Sucigaba Ba, "Idan Kayi Ciyaman Addu'ar Yacigaba Sai Allah Ya Amsa Sai Yazama Gwamna Sai Kawai Yadaukoka Yabaka Shugaban Masu Yad'a Karyarsa (Mai Taimakamasa Wajen Yad'a Labarai) To kai A Ganinka Kai Dashi Duk Kunci Gaba Duk Kuwa Da Cewa Barna Kuke Tafkawa Da Sace Dukiyar Jama'a Kunbar Al'umma Acikin Kuncin Rayuwa Ba Ruwanku Da Damuwarsu Sai Abinda Kukeso Shine Kawai Zakuyi".

Mufadawa Shugabanni Gaskiya Koda Kuwa Basaso Wannan Shine Tsantsar Soyayyarmu Garesu Bawai Kokarin Karesu Ba.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: