Friday, 17 May 2019
Dalilin Da Ya Sa Nake Auri-saki – Adam Zango

Home Dalilin Da Ya Sa Nake Auri-saki – Adam Zango
Ku Tura A Social Media

 Fitaccen jarumin nan na dandalin shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Adam A Zango wanda aka fi sani da Prince Zango ya bayyana dalilin da ya sa yake yawan auran mata kuma daga bisani ya rabu da su. Jarumin ya bayyana cewa ba wai baya iya zama da mace bane, sai dai

"ba zan iya fada muku abin da ya hada shi da matata ta farko, da matata ta biyu da kuma matata ta uku ba."

 “Allah yana hada mata, mace da namiji. Allah ya halicci mata domin su kasance ni’ima a garemu maza. Don mu Allah ya halicce su." 

Adam ya kuma bayyana cewa Allah ya rigada ya tsara ma mutum kaddararsa da abunda zai faru da shi tun kan a haifasa har izuwa ranar da zai amsa kiran mahallicinsa.

Dan wasan ya bayyana hakan ne a hira da yayi da shafin BBC Hausa inda yake cewa:
 "Allah Ubangiji ya rubuta wa mutum abin da zai faru da shi tun daga farkon haihuwarsa har zuwa ranar mutuwarsa." “Kuma wannan kaddarar da Allah yayi mun itace tawa, saboda ni , Allah yana gani, Allah ya ba ni komai da na roke shi, amma ban da mace wanda nake zaman aure da su.

 “Sannan kuma ina so na gayawa mutane wani abu cewa, duk mutin da ya kasance zai yi aure ya rabu da mace, ya kara yi kuma ya kara rabuwa da ita, toh ya kamata su gane cewa wannan mutumin ba mazinaci ba ne. Saboda ni Adamu Zango Allah ya ba ni, duk duniya a cikin masana’antar Kannywood, babu wanda mata ke so iri na. Toh me zan yi da aure?”

Share this


Author: verified_user

0 Comments: