Friday, 24 May 2019
Ana biya na naira 180 ana saduwa dani - Fatmata Kanu

Home Ana biya na naira 180 ana saduwa dani - Fatmata Kanu
Ku Tura A Social Media


A wata hira da manema labarai suka yi da wasu 'yan mata guda biyu a kasar nan masu suna Mariam da Fatmata sun bayyanawa manema labaran yadda ake saduwa da su a kowanne kwana daya inda ake ba su Leone 5,000 wato kimanin naira 180 a kudin Najeriya.

Ga yadda hirar ta su ta kaya da Fatmatu Kanu, 'yar shekara 18 a duniya:

"Babu yadda zan yi na ci abinci idan ban fita na nemi maza a titi ba, maza suna cewa suna bukata ta, sukan kaini gidajensu inda suke kwanciya dani gaba daya ranar sai su bani Leone 5,000, wato kimanin naira 180.

"Inda mahaifiyata ba ta mutu sanadiyyar Ebola ba, da ban shiga wannan harkar ba. Daga karshe ba ta samu ta yi komai ba, ko magana ba ta iya yi."

Fatmata ta ce tana saduwa da maza bakwai zuwa takwas a dare daya.
"Wasu lokutan muna yin jima'in minti biyu domin samun Leone 5,000 wato naira 180, sannan farashin yana kai wa Leones 50,000 wato naira 1800.

"Ina da kanne guda biyu, kuma ni ke kula da su, idan na fita na samu kudi, ni nake biya musu kudin makaranta.
"Ina so na yi karatun likita na bangaren masu karbar haihuwa, wannan shi ne fatana tun ina yarinya karama."
Hasashe ya nuna cewa kimanin mata 300,000 ne ke karuwanci a kasar Saliyo.

Wata da manema labaran suka yi hira da ita mai suna Mariama Fofanah, 'yar shekara 20 a duniya, ta bayyana yadda ta fara harkar karuwanci:

"Ina 'yar shekara 14 na fara karuwanci, mahaifiyarmu ce ta sanya mu a cikin wannan hali saboda ba ta iya kula damu. Tana yawan cewa mu shegu ne.

"Akwai wani lokaci a baya da na samu wani mutumi mun yi ciniki da shi sosai. Bayan ya gama saduwa dani, sai ya ki ba ni kudina, sai ya gudu da kudina da kuma wayata. Nayi kokarin rigima dashi, sai ya doke ni a fuska, inda ya ji mini ciwo sosai ya gudu kuma."

Kungiyoyin ba da agajin gaggawa sun ce ana kara samun karuwai a kasar tun barkewar cutar Ebola.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: