Tuesday, 28 May 2019
An kama kanin sakataren Gwamnatin Zamfara Buhunan kudi

Home An kama kanin sakataren Gwamnatin Zamfara Buhunan kudi
Ku Tura A Social Media


Hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta kama wani mutumi mai suna Murtala Mohammed dauke da buhunan kudi guda hudu makare da naira dubu daya daya har naira miliyan sittin a jahar Zamfara.

Legit.ng ta ruwaito wannan mutumi kanine ga sakataren gwamnatin jahar Zamfara, Farfesa Abdullahi Shinkafi, kuma EFCC ta samu nasarar kama shine bayan samun bayanan sirri game da zarginsa da ake yi da safarar makudan kudade. Hukumar EFCC ta yi caraf kanin sakataren gwamnatin Zamfara da naira miliyan 60
  Jami’an EFCC sun samu wannan nasara ne a ranar Talata, 28 ga watan Mayu na shekarar 2019 a yayin da suka kai samame wani gida da Murtala yake zama dake lamba 145 a rukunin gidajen Igala, a saman babban hanyar garin Gusau jahar Zamfara.Hukumar EFCC ta yi caraf kanin sakataren gwamnatin Zamfara da naira miliyan 60 Source: UGC Daga cikin abubuwan da jami’am EFCC suka kama akwai wata motar Toyota Land Cruiser Prado baka, dake da lamba DKA 67 PX Kaduna, a cikin motar aka samu jakkunan buhu na Ghana Must Go guda hudu dauke da yan dubu dubu, kowannensu na dauke da naira miliyan goma sha biyar biyar, jimilla miliyan 60.
Haka zalika jami’an EFCC sun gano bindiga mai baki daya dake cike da alburusai, karamar bindiga guda daya kiran gida, da kuma alburusai guda talatin da bakwai. Daga karshe hukumar tace zata gurfanar dashi gaban kotu da zarar ta kammala gudanar da bincike.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: