Thursday, 11 April 2019
Wata sabuwa ! Shahararren Darakta Abdulmumin Ilyasu Tantiri Ya Fice Daga Kannywood

Home Wata sabuwa ! Shahararren Darakta Abdulmumin Ilyasu Tantiri Ya Fice Daga Kannywood
Ku Tura A Social Media

Fitaccen jarumi kuma mai bada Umarni Iliyasu Abdulmumini wanda ake yi lakabi da 'Tantiri' ya bayyana cewa ya fita daga  cikin masana'antar shirya Finafinan Hausa, saboda rashin gamsuwa da shugaban na masana'antar. Tantiri ya bayyana ficewar sa ne a shafin sa na Instagram. Ga abin da ya rubuta @abdul_ilyas_tantiri :

"Assalamu alaikum,Ni ABDULMUMIN ILYASU MAISANGO ina sanar da ficewata daga cikin masana'antar KANNYWOOD Saboda Rashin gamsuwa da shugabancin wannan masana'anta baki daya,tareda wasu dalilai da suka shafeni.Bissalam NAGODE."

Kafin ficewar sa dai, jarumin yana daya daga cikin jaruman da suka fara suna a masana'antar Fim tun farkon kafata. Sannan ya bada gaggarumar gudummuwa a harkar, ya kuma shirya tare da bada umarnin manyan Finafinai.
Share this


Author: verified_user

0 Comments: