Monday, 15 April 2019
Tunda Azumin Ramadan Ya Karato Ina Neman Gafarar Al'umma - Adam A Zango

Home Tunda Azumin Ramadan Ya Karato Ina Neman Gafarar Al'umma - Adam A Zango
Ku Tura A Social Media


ya daga cikin taurarin masanaantar shirya fina finan Hausa, na Kannywood,  Adam A Zango,  yace tunda Allah yasa Azumin watan Ramadana ya karato yana bukatar Yafiyar Al'umma.

Ya fara da Sallama ne irin ta Addinin Musulunci kafin ya tafi kai tsaye zuwa ga sakon neman yafiyar hakan na kunshe cikin wani faifayin bidiyo daya wallafa a shafin sa Wanda ya dauka a cikin fantsamemen gidan daya gina.

A baya bayanan an kai ruwa rana a tsakanin Adam A Zango da kuma sarki Ali Nuhu, bisa wani batu na daban da su suka san shi,  wanda hakan ya jawo zage zage karshe ma suka yada zango a Kotu.

Har ila yau Jarumin yasha yarfa magana mai baki biyu a dukunkune, ciki harda bakaken maganganu,Sai dai MOPPAN tayi nasarar sasanta Manyan Jaruman.

Yanzu haka dai Zango ya bukaci ya yafe masa dukkan kurakuren da yayi tunda a Azumi nan yazo.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: