Thursday, 4 April 2019
Tabbas Ali Nuhu Ya Cika Dattijo (karanta)

Home Tabbas Ali Nuhu Ya Cika Dattijo (karanta)
Ku Tura A Social Media
ALI NUHU YA CIKA DATTIJO
Daga shafin @ali_nuhu_fans_club
Ban taba yin martani ga wani ko wata yayi reposting ba. Koda kuwa nayi martanin ne domin kare mutuncinsa.
Bai taba nuna goyan bayansa akan martanin da nayi ga wani ko wata ba, a maimakon hakanma sai sai ya kwabe ni ko ya haneni a lokutan da yaga abin zai kazanta.

Bai taba Zama dani yaci mutuncin wani ko wata ba, ko kuwa yayi munafuncin wani ko wata ba. Kullum tunaninsa akan cigabansa, wadanda suke kewaye da shi da Kuma masana'antar a jumlace.
A farkon shekarar da ta gabata wani a masana'antar ya taba yi masa kazafi damu masoyansa. Har nayi dukkan shirye shiryen Kai wannan mutum ajiya a kurkuku Amma wannan bawan Allah ya lallashe ni. Na Kuma janye kudurina.

Na dade Banga mai hakurin wannan bawan Allah ba. Tabbas ka cika DATTIJO.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: