Monday, 8 April 2019
Ta sake kacamewa tsakanin Ali Nuhu da Adam A. Zango: Adam ya zargi Ali Nuhu da sa yara su ci mutuncin mahaifiyarshi, ya rama da zagi: Shima Alin ya mayar da martani

Home Ta sake kacamewa tsakanin Ali Nuhu da Adam A. Zango: Adam ya zargi Ali Nuhu da sa yara su ci mutuncin mahaifiyarshi, ya rama da zagi: Shima Alin ya mayar da martani
Ku Tura A Social Media
Ga dukkan alamu dai rikici ya sake bayyana karara tsakanin manyan taurarin fina-finan Hausa, Ali Nuhu da Adam A. Zango. An jima ana ganin alamar hakan a cikin sakonnin da Adamun ke sakawa a shafukanshi na sada zumunta saidai a yanzu ya fito karara ya kira sunan Ali Nuhu inda ya zargeshi da sawa a ci zarafin mahaifiyarshi.
Adamun ya zargi Ali Nuhu da sa yaranshi su ci zarafin mahaifiyarshi, inda yace, wane sauran mutunci gareni a Kannywood? Ko ni dan zinane ba za'a zagi mahaiyata in kyale ba, sannan shima ya zagi Ali Nuhun ya kuma ce karsu fasa kasheshi.


Saidai ga dukkan alamu wannan fadan yazo da sabon salo, domin ada idan ana fada da Ali Nuhu yakan yi kira da cewa kada wanda ya shigar masa sannan shi ma bazai mayar da martani ba.
Amma a wannan karin yayi wani rubutu wanda yake alamta cewa shima wannan karin a shirye yake. Alin dai ya rubuta cewa, An zo wajan, duk da dai da dama na kira a gareshi da kada ya biye.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: