Saturday, 13 April 2019
Shin Da Gaske Ummi Zeezee Ta Kira Hadiza Gabon Yar Madigo ?

Home Shin Da Gaske Ummi Zeezee Ta Kira Hadiza Gabon Yar Madigo ?
Ku Tura A Social Media
A kwanakin bayyani ina fatan kunga irin rubuce rubuce da sunkayi yawo a social media musamman facebook ana cewa ummi zeezee ta kira Hadiza gabon yar lesbian.
Ga jawabin Ummi zeezee daga shafinta na instagram.

"Salam jama'a.dangane da rigimar hadiza Gabon da amina amal ni ba ruwana aciki ban kuma ce zansa a miyar da hadiza Gabon kasarta ba sannan ban kuma kirata da cewa tabbas ita yar lesbian bace domin ban taba kamata ido da ido tanayi ba .wannan sharri ne kawai wasu suka hada hotona da hadiza Dana amal suka kuma rubuta cewar nayi wannan maganganun.na lura da cewa akwai wasu kananan marasa kunya matsorata in suna son su fadi wata maganah akan wani kuma suna tsoro sai su nemi hotona suyi rubutu suce nina fada dan sunsan ni mace ce marasa tsoro zan iya maganah akan kowa ba tare da shakka ba.dan haka in ma zansa baki a rigimar hadiza Gabon da amina amal to silhu zan musu a matsayina ta wacce ta girmesu a harkar fim bawai in sake lalata maganah ba dan kannena na daukesu .musamman ita hadiza Gabon tana ban girma sosai ko sunana ban taba jin ta ambata kai tsaye ba sai dai ta kirani da "BIG SIS " dan haka ni duk mai ban girma a rayuwa to ina bawa wannan mutumin daraja na musamman nagode.daga UMMI IBRAHIM BAGUDDIRE."


Share this


Author: verified_user

0 Comments: