Wednesday, 3 April 2019
Priyanka Chopra Na Shirin Kashe Aurenta

Home Priyanka Chopra Na Shirin Kashe Aurenta
Ku Tura A Social Media
Wata Mujallar Amurka ta labarto cewa; shahararriyar ‘yar fim din Indiyar nan wato Priyanka Chopra da mijinta Nick Jonas sun shirya tsaf domin rabuwa tare.
Priyanka Chopra da mijinta Nick Jonas ba su da lokacin juna a matsayin ma’aurata shiyasa suka yanke shawarar rabuwa kawai. Kamar yadda Mujallar ta tabbatar.
A cewar Mujallar, ‘yar fim din mai shekaru 36 da mijinta mawaki mai shekaru 26, sun yi saurin fara soyayya ne, sai da kuma suka yi aure, sannan suka fahimci juna.

Rahoton ya yi nuni da yadda ma’auratan suke fada akan komai wanda ya shafi aiki, kasancewa tare. Sannan wani abin shi ne yadda ita Priyanka da mijinta Nick suke saurin fadawa abu, wanda wannan ne ya haifar musu da abin yak e shirin aukuwa a yanzu. Domin sun fara soyayya ne ba za ta kuma suka yi aure nan da nan.
A cewar majiyar ta mu, ta bayyana cewa Nick ya dauka ‘yar fim din natsattsiya ce mai kuma fahimta bayan sun yi auren, sai yanzu ne bayan sun yi aure ya fahimci yadda take da saurin yin fushi.
A cewar majiyar tamu ta labarto cewa ‘yan’uwa da iyalan Nick ne suka nemi da ya rabu da ita kawai. Domin a cewarsu da da farko sun dauka Priyanka ta yi hankalin da za ta natsu wuri guda har ta samu ‘ya’yanta. Sai yanzu suka fahimci cewa ‘yar shanawa ce da take nuna kamar shekarunta ba su wuce 21 ba.
Har wala yau majiyar ta ce; rabuwa kuma suna ganin yana da alaka da kudi. “Sun yi saurin yin aure ba tare da tsayawa sun fahimci juna ba.” Inji majiyar.

Ma’auratan sun yi aure ne a Indiya cikin watan Disambar shekarar da ta gabata. Inda Piriyanka da Nick suka kwashe kwanaki 3 ana hidimar biki, a fadar Jodhpur na Masarautar Umaid Bhawan. Inda kowannensu ya yi rantsuwar aure da addininsa. Inda ita Hindu ce, mijinta kuma Kirista ne.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: