Wednesday, 10 April 2019
Mahangar Dokokin Nijeriya Game Da Rikicin Hadiza Gabon Da Amina Amal - Daga Barista Abba Hikima

Home Mahangar Dokokin Nijeriya Game Da Rikicin Hadiza Gabon Da Amina Amal - Daga Barista Abba Hikima
Ku Tura A Social Media

Daga Barista Abba Hikima

 Duk da ba na kallon Hausa films Sosai kuma ban san da yawa daga cikin su ba. Amma abun da naga Hadiza Gabon ta yiwa wata mai suna Amina Amal, bai kamata ba kuma ya sabawa kundin laifukan 'yancin Dan Adam ta Fuskoki 3.

Criminal case: Wato Manyan Laifuka, Za'a iya cajin Hadiza Gabon, a karkashin sashuka da dama na kundin laifuffuka domin yin amfani da karfi, tsoratarwa, hadin baki, duka da sauran su kuma hakan zai iya bayuwa ga daure ta a gidan yari na tsawon shekaru.

Torturing: Hadiza Gabon, na iya fuskantar biyan diya mai yawa saboda takurawa Amal da cin zarafinta da ta yi a karkashin tortuous wrong redresses.

Violation of fundamental human rights: Haka kuma abun da aka yiwa Amal ya sabawa kariyar da dokokin kare hakkin Dan Adam suka tanada a Najeriya.


Saboda haka ya kamata hukumomi su shiga cikin wannan magana da gaggawa domin taimakawa wannan yarinya.

Me za Ku ce?


Sources:JARIDAR DIMOKURADIYYA:

Share this


Author: verified_user

0 Comments: