Monday, 15 April 2019
Jaki Ko Taiki Wanne Ya Dace A Buga ?

Home Jaki Ko Taiki Wanne Ya Dace A Buga ?
Ku Tura A Social Media

Daga Datti Assalafiy

Rubutun karshe akan wannan dambarwa.
Ga masu ganin cewa rashin adalci ne rubutun da akayi akan Amina Amal aka kyale Hadiza Gabon, domin itama ai ba 'yar Nigeria bace, kuma ko videon daya bayyana ya isa ya tabbatar cewa da ita gabon din da yarinyar (Amal) duk kwaryar sama ke dukan ta kasa, saboda me za'a daki jaki a kyale taiki,? wasun su har cewa suke" kodai muna tare da Habon ne? wai nawa ta biyanmu muka batawa Amal suna?

Ko kadan masu wannan magana basu yi mana adalci ba, domin kuwa bamu da alaqa da wata Hadiza gabon kuma bama son alaqa da ita dama irinta, rubutu kuma tun asali bamu yi shi domin videon da ake magana ba, munyi ne domin jan kunne ga ita yarinyar, domin kaf cikin wadan nan 'yan kannywood din babu yarinyar dake cin karanta danye fiye da ita, babu yarinyar dake tsokanar Allah da manzon shi S.A.W a bainar jama'a kamar ta.

Watan azumi watan rahama da ibada watan da kowa ke komawa ga mahalicci, amma a watan azumin daya gabata kowa zai shaidi yadda yarinyar nan ta dinga yada hotunan tsiraicinta wa duniya da niyyar tsokanar addinin musulunci, amma a lokacin bamu kausasa harshe a kanta ba, munyi zaton zata daina ko kuma masu ruwa da tsakin masana'antar ta zasu dauki mataki, maimakon dainawa sai muka ga abun kullum kara gaba yake. To dama kowa yasan Zuma sai da wuta.
Don haka muka yi Ijtihadin cewa babu wata maslaha ga sha'anin wannan yarinyar sai fitowa ayi mata tonon silili a kuma ja mata kunne da kausasash-shiyar murya idan ba haka ba ba'a san inda abun nata zai tsaya ba, ba'a san mutanen da zasu tasirantu da hakan ba.

Wannan shine dalilin da yasa mukayi rubutun da mukayi a kanta, mu da kanmu bama son tona asirin musulmi domin hakan babu kyau, amma Allah shine shaidarmu idan munyi hakan domin gyara ko domin wata manufa ta daban, saboda haka ban ga dalilin da za'ace itama gabon sai anyi mata tonon silili anci mata mutunci ba, saboda me za'ayi mata? me zamu amfana dashi? Alhalin dabi'armu ta sa'ba da cin mutunci, shin laifinta yakai ayi mata hakan? duk da bama ra'ayin wadan nan mutane hakan bazai saka su kasa samun adalci daga garemu mu dinga hawa kan mai uba da wabi ba, Bari zaku yi itama Hadiza gabon ta dauki layin Amal kuma taki daukar nasiha, a sa'ilin zaku ga yadda zamuyi mata figar kazar bakar mahaukaciya, domin ita din ma muna da abin fadi akanta.

Kuma koda ta tabbata zargin lesbian din da ake mata gaskiya ne ni bani da matsala da hakan, taje ita da ubangijinta, tunda a boye take yi kuma tana jin kunyar mutane su san tana aikatawa, sannan akwai dubbun masu aikata hakan a lungu da sako na arewacin kasar nan amma tunda a boye suke aikatawa za'a iya saka musu ran tuba da kuma samun yafiyar ubangiji sa'banin ita waccan Amal din mai bayyana laifukanta a bayyanar Jama'a.

A karshe dai muna nasiha ga wadan nan yara dama abokan sana'arsu da suji tsoron Allah, duniyar nan bata da tabbas wanda yayi da kyau ma yaya yake karewa ? akwai da yawan matan da suka fiku kyau, kudi, diri, sun aikata abinda suka so a baya, amma yanzu sun sami kansu a yanayin da basa so. Duniya tayi musu atishawar tsaki, domin duk abinda mutum ya shuka shi yake girba, ina ma zaku taimaki kanku kuyi aure ku zauna a gidajenku ku bautawa Allah, sai ku sami mai kyau a duniya da lahira. wanda ya wallafa rubutun Malam Aliyu Imam Indabawa.

Allah Ya shirya.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: