Wednesday, 3 April 2019
Gwamnatin jihar Zamfara zata dauki matsafa 1,700 domin fuskantar Kalubalen tsaro a jihar.

Home Gwamnatin jihar Zamfara zata dauki matsafa 1,700 domin fuskantar Kalubalen tsaro a jihar.
Ku Tura A Social Media

Daga Haji Shehu

Kwamishinan kananan Hukumomi na jihar Zamfara Alhaji Bello Dankande, yace a Yunkurin gwamnatin jihar na daidaita matsalar tsaro, gwamnati na shirin daukar matsafa 1,700 domin gauraya su da yan Kato da gora (CJTF) guda 8,500 da yanzu haka gwamnatin ke da su.

Alhaji Bello Dankande ya shaida hakan ne bayan ganawar da sukayi akan sha’anin tsaro tare da Sarakunan gargajiya da Shugabannin kananan Hukumomi da kuma shugabannin Fulani yau a birnin Gusau.

Ya kara da cewar “Kowacce masarauta cikin masarautu 17 da muke dasu, zamu dauki matsafa 100 mu kara akan yan Kato da Gora  500 da muke dasu a kowacce masarauta.

“Za kuma mu dauki wasu masu sanya ido akan gidajen seida manfetur domin dakile masu yiwa yan ta'adda safarar manfetur zuwa Daji.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: