Tuesday, 9 April 2019
AUDIO : Hirar Habibu Nakasari Da Yan Jarida

Home AUDIO : Hirar Habibu Nakasari Da Yan Jarida
Ku Tura A Social Media

ABINDA AKA YIWA WANNAN BAWAN ALLAH TA'ADDANCI NE
AUDIO : HIRAR DA HABIBU NAKASARI
Tun jiya da daddare na karanta wannan labarin a jaridar Rariya wasu azzalumai sun shiga gidan su wannan bawan Allah mai suna Habibu dake unguwar Nakasari cikin birnin Sokoto suka guntule mishi hannunsa guda biyu kuma suka gudu
Wannan labarin ya na da matukar tayar da hankali, dare daya suka yiwa wannan bawan Allah kisan tsaye, abinda aka masa bashi da maraba da ayyukan ta'addanci
Kwanaki ma an samu abu makamancin haka da ya faru a Sokoto inda wasu 'yan bangar siyasa suka guntule hannun wani bawan Allah guda daya
Me yake faruwa ne a jihar Sokoto abar alfaharin mu?
'Yan uwa matasa a dinga zama da shiri, dokar Kasar Nigeria ta bada dama akwai self defence, haka kawai kana zaune wasu suzo su ma ta'addanci sai kace kabewa? wannan kuskure ne gaskiya
Allah Ka tona asirin wadanda suka aikata wannan ta'addanci Amin.
DOMIN SAURARIN HIRAR KUYI AMFANI DA WANNAN LINK


Share this


Author: verified_user

0 Comments: