Sunday, 14 April 2019
Aski Yazo Gaban Goshin Nafisa Abdullahi Zata Shiga Sahun Ma'aurata

Home Aski Yazo Gaban Goshin Nafisa Abdullahi Zata Shiga Sahun Ma'aurata
Ku Tura A Social Media
Wannan wani masoyin tauraruwar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi ne da ya hada hotonshi dana jarumar saboda irin soyayar da yake mata har ya nuna alamar kamar an kusa daura musu aure.

Wannan hoton da ya saka ya dauki hankulan mutane sosai inda akaita cece-kuce musamman idan aka lura da madubin dake bayanshi babu Nafisar, ta haka wasu suka rika mai tsiyar cewa Aljanace ya rike wasu kuma suka rika cewa sun ganoshi hada hoton yayi amma shidai ya hakikance cewa yana son Nafisarne.

A nata martanin, Nafisa Abdullahi yayin da wata ta tambayeta ya akai ba'a ganta a madubin dake bayan hoton ba? Tace itama abin ya isheta.Share this


Author: verified_user

1 comment: