Tuesday, 30 April 2019
Aji-No-Moto Ya Bayyana Maryam Booth A Matsayin Babbar Jakadiyarsa

Home Aji-No-Moto Ya Bayyana Maryam Booth A Matsayin Babbar Jakadiyarsa
Ku Tura A Social Media


West African seasoning company (WASCO), Wanda aka fi Sani da ajino moto, ya bayyana shahararriyar jarumar kannywood Maryam Booth, a matsayin sabuwar jakadiyar kamfanin a Arewacin Najeriya.

Bayanin hakan na zuwa ne a wajen Taron da ya Gudana Wanda akayi a kano yau din nan Wanda ya dau hankalin wakilan 'Yan kannywood din da suka Halarci Taron.

Yayin da yake jawabi a gun taron manajan  dakartan WASCO Mr. Niki junichi, ya bayyana cewa an Samar da Magin Ajino, a kasuwannin Najeriya tun shekaru 30 da suka gabata.

Ya Kara da cewa Wannan dalilin ne Yasa aka zabo jarumar a Arewa, domin hakan zai kara taimakawa wajen bayyanar da Wannan Magi na Ajino, Kazalika ya kara wuce sa'a.

Yace kamfanin zai ci gaba da habbaka tattalin arzikin Najeriya da kuma kara samun gamsuwa  da ingancin sa.

A nata bangaren Maryam Booth, yayin jawabin godiya tace duk da kamfanin yana da 'Yan gasa da yawa tace za ta yi iya kokarin ta domin zama ta gaba a cikin su.

Zan Himmatu wajen bada gudummawa Musamman a Bangaren ilimantarwa, nishadantarwa ta yadda zai kara zama lamba daya a Duniya.

Tace, Zata iya tunawa yadda jarumar barkwancin nan Helen Paul, da tsohon babban Yaya Naija housemate, chief Miyosun Amosu, suka zama jakadun shekarar bara a jahar legas.

Wana Fata za Ku Ma ta?

Share this


Author: verified_user

0 Comments: