Friday, 26 April 2019
Adam A Zango Yayi Aure Na Shida Kalli Kyawawan Hotunan sa Da Amaryasa

Home Adam A Zango Yayi Aure Na Shida Kalli Kyawawan Hotunan sa Da Amaryasa
Ku Tura A Social Media
Tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango kenan da Amaryarshi, Safiya da aka daura musu aure yau. Rahotanni sun nuna cewa aurenshi na shida kenan. Wannan na zuwane kasa da sati daya bayan da Adamun ya bayyana cewa an daga aurenshi sai bayan sallah.A sakon daya fitar ta dandalinshi na sada zumunta, Adamun ya godewa masoyanshi da suka aikemai da sakon taya murna, inda kuma yayi fatan cewa in Allah ya yarda shi da matarshi har abada.
Muna tayasu murna da fatan Alheri.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: