Monday, 8 April 2019
Abun da yake bani tsoro ! Duk Yarinyar Da ka Gani A Kannywood Sai Tace Ali Nuhu Ne Ya Kawo Ta

Home Abun da yake bani tsoro ! Duk Yarinyar Da ka Gani A Kannywood Sai Tace Ali Nuhu Ne Ya Kawo Ta
Ku Tura A Social Media


Daga Fulani Shuaibu

JARIDAR DIMOKURADIYYA:Babban Abun da yake bani tsoro wani lokaci ya saka in zubar da hawaye shine, mafi yawancin Jarumai Mata na masanaantar shirya fina-finan Hausa na Kannywood,  idan ana hira da su game da yadda Jarumar ta sami kanta a masanaantar sai tace Jarumi Ali Nuhu ne yayi mata hanya zuwa masanaantar.

Daga cikin su akwai Halima Artete da Nafisa Abdullahi da Rahma Sadau,ita kuwa Maryam Yahaya ma cewa BBC Hausa tayi har gidan su Jarumi Ali Nuhu yaje ya karbo ta a gaban Iyayen ta, kuma ba su kadai ba.

Kuma Jaruma Mata idan suka shigo masanaantar, sai kaga ba a sana'ar shirye-shiryen Fim din suka tsaya ba sai kaga sun shiga wani layi na daba, kaicho.

Nayi Imani da Allah indai har masu karanta wannan sharhin nawa zasu yi mun adalci zasu tabbatar da magana ta harma su gasgata ta idan suka kalli Jarumai mata lokacin suna sababbin shigowa harkar da kuma idan sun kwana biyu.

Wannan labari yana bani tsoro to yanzu shi Ali Nuhu a wane matsayi yake kenan? Yadda fa ake tambayar matan nan a duniya suna cewa Ali ne ya kawo su harkar Fim haka fa zasu maimaita a Lahira.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: