Wednesday, 27 March 2019
Yadda Zaka Samu Kyautar Sama Da 4GB A Layin Airtel

Home Yadda Zaka Samu Kyautar Sama Da 4GB A Layin Airtel
Ku Tura A Social Media


Wannan wata dama ce ta samun garabasar Kyautar data da masu amfani da layukan airtel zasu iya morewa. Hakan yana samuwa ne ta hanyar damar da Airtel suka baiwa masu amfani da network dinsu wajen dawo da kudin da suka siyi data zuwa yadda suke.
“Data reversal” shine tsari da kamfanin airtel suka fito dashi, tsarin da ke baiwa mutum damar dawo da kudin da yayi amfani da su wajen siyan data ta browsing.

A duk lokacin da ka sayi data, akwai bonus da airtel ke bayarwa na data wacce ita ce zasu fara tabawa a yayin da ka fara browsing kafin suzo kan ainihin data daka siya da kudin naka. To a nan ne shi wannan tsari na “reversal” yake iya yiwuwa.
Ta yaya zan iya more wannan garabasa ta airtel?
Da farko dai kana da bukatar ka samu sabon layi na airtel 4G SIM.
Sai ka sanya kati kamar na N1,000 sai ka sayi data ta N1,000. Zasu baka 1.5GB sannan su baka bonus na data wanda dashi ne zaka fara browsing din.
Idan baka shiga cikin 1.5GB na data din da ka siya ba(ma’ana idana ya kasance da bonus din kake amfani), bayan awa ashirin da hudu(24hours), zaka iya dawo da kudinka ta hanyar danna *121*6#.

Bayan ka dawo da kudin naka kuma zaka iya sake siyan data dasu wanda anan zasu kara baka bonus na data ta browsing, bayan awa 24 zaka iya sake dawo da kudin naka sannan ka kara yin sub din har zuwa iyakar iyawar ka.
Zaka iya duba yawan datar taka ta hanyar dannan *223# ko kuma *140#.
Kunga kenan a wannan tsari, zaka iya daukar lokaci mai tsawo kana amfani da bonus na data ba tare da ka rinka sanya kati akai-akai ba.
Ku tura ma abokanen ku dake kan Facebook, Whatsapp da sauransu…

Share this


Author: verified_user

0 Comments: