Sunday, 3 March 2019
Sheikh Al-Mannar Ya Nesanta Kansa Akan Takardar Hana Sheik Dahiru Bauchi Tafsiri

Home Sheikh Al-Mannar Ya Nesanta Kansa Akan Takardar Hana Sheik Dahiru Bauchi Tafsiri
Ku Tura A Social Media

Daga Ibrahim Ammani Kaduna

Babban Limamin Masallacin Juma'a na Al Mannar dake Unguwar Rimi GRA Kaduna Sheikh Tukur Adam Al- Mannar, ya nesanta kanshi dangane da wata takarda dake yawo a kafafen sadarwa na zamani cewar, wai wata kungiya ta Ahlus Sunnah ta gana da gwamna El Rufa'i, inda ta gindaya wasu sharuda ga Gwamnan kafin su goyi bayan shi, daga cikin yarjejeniyar wai har da batun hana Sheikh Dahiru Bauchi gudanar da Tafsiri a Kaduna.

Sheikh Al Mannar ya kara da cewar ya kadu sosai lokacin da yaga wannan takarda ta karya wacce aka jingina ta a gareshi, kuma a iyaka sanin shi babu wata kungiya mai wannan suna na Majalisar Ahlus Sunnah a Kaduna, sai dai wadanda suka kirkiri wannan labarin na karya sun shirya shi ne domin wata muguwar manufa da burin bata sunan shi da haifar da rudani a cikin al'umma.

Malamin yayi addu'a ta tsinuwa da narkon azaba ga dukkanin wadanda ke da hannu wajen shirya wancan takarda ta karya da yadata tsakanin jama'a, tare da fatan Allah ya hana musu samun biyan bukatun su duniya da lahira.

Malamin yayi wadannan bayanai ne a zantawar da yayi da wakilin mu ta wayar tarho a daren jiya.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: