Thursday, 21 March 2019
Nafisa Abdullahi ta bayyana dalilin da yasa bata yi wa kowane dan siyasa yakin neman zabe ba

Home Nafisa Abdullahi ta bayyana dalilin da yasa bata yi wa kowane dan siyasa yakin neman zabe ba
Ku Tura A Social Media


Tauraruwar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi ta bayyana dalilin da yasa bata shiga tawagar abokan aikinta ba wajan tallata wani dan takarar siyasa ba, Nafisa ta bayyana hakane ta shafinta na dandalin Twitter a yayin amsa tambayoyi da tayi daga Kannywoodscene.

Nafisar tace, bata son ta tallata dan takara ta sa masoyanta su zabeshi alhali kuma tun asalai ba shine ra'ayinsu ba.
Da aka tambayeta shin wa take goyon baya tsakanin gwamna Ganduje da Abba a zaben Kano,Nafisa tace ba abune da zata gayawa Duniya ba.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: