Wednesday, 20 March 2019
Muhimmin Sako na zuwa ga yan uwana talakawa! Akan Yan Siyasa - Daga Nura m Inuwa

Home Muhimmin Sako na zuwa ga yan uwana talakawa! Akan Yan Siyasa - Daga Nura m Inuwa
Ku Tura A Social Media
Zaifi mana kyau mu rage zakewa a cikin harkar yan siyasa, domin haka yana jawo mana matsala a tsakanin yan uwan mu wanda su ba haka suke da nasu yan uwan ba. Kuyi duba da wasu abubuwa kune kuke gaba su basayi, kune kuke kiyayyar kawunan ku da gaske su basayi, karshe ma sunce bata da makiyi na din din din. Sannan duk hassadar da za kuji suna yiwa juna abu daya ke rabasu ba kishin jama'a bane jam'iya ce. Duk nagarta da aikin da zakayi bai hana su kusheka indai kun raba jam'iya, haka duk tabargaza da rashin mutunci da tauye hakkin al'umma da wanin su zaiyi yana shiga jam'iyar dake adawa dashi za kaji an wanke shi fes sai ka zata waliyi ne. Sannan matsalolin dake faruwa kasarka tun daga kan boko haram ban taba jin ance bomb ya tashi da wani gwamna, dan majalisa ko ciyaman ba ko 'Ya'yansu, saboda suna da kariya amma manyan malamai nawa kaji an harbe ? hafizai nawa bomb ya tashi dasu ??

wanda ka sani da wanda baka sani ba. Dan talaka kuwa ba wanda ya isa ya kimanta adadin wa danda suka mutu duk da haka mun kasa yin tunani mu gane daga ina matsalar take. Yau an wayi gari ana satar mutum kuma banji an saci daya daga cikin su ba saboda tsaron dake biye da su 'ya'yansu, bbu mai ganin su bare ya kama. Ana satar 'ya'yan marasa karfi da talaka mai neman na abinci a hanya yau su ake kamawa ake neman kudi a gurin su saboda su bbu tsaro a tare da su, duk masifar da ta tawo kan talaka take karewa amma shi talakan ina tunanisa ya tafi🤔🤔 Abun takaicin da nakeji an saci malami kwanan nan inda dalilin da ya jawo hakan bai huce siyasa ba, watakila da ba'a ganshi cikinsu ba da bbu ruwan su dashi, duk da matsayin sa cikin al umma yafi nasu amma sun gaza bashi tsaron da yafi na su, Yadda shima baza'a iya yin garkuwa dashi ba,kamar  yadda suka gagara ayi da su da Iyalansu. Don hka Talaka don ALLAH ka guji zakewa akan harkar yan siyasa domin tsira da lafiyar ka, ka mayar da  lamarin ka ga ALLAH ya kawo maka sauki kan duk abun da ya dameka, idan rashi ne bbu mai maka maganinsa sai ALLAH, wani lokacin ma rashi na taimakon mutum wajan tunawa da ALLAH tunda duk iskancin mutum yana rasa lafiya yake fara tuna ALLAH saboda tsoran mutuwa. Dan ALLAH muyi wa k

Share this


Author: verified_user

0 Comments: