Uncategorized

Kurakuren Da Ma’aurata Ke Aikatawa Yayin Jima’i (saduwa)

Akwai abubuwa da yawa wadanda Ma’aurata suke aikatawa alokacin Jima’insu. Kuma wadannan abubuwan suna da illoli masu yawa dangane da lafiyarsu jikinsu ko addininsu. Ga wasu ‘yan kadan Zan lissafo:

1. Rashin gabatar da wasanni kafin Jima’i : wannan ba daidai bane domin kuwa Manzon Allah (saww) yace “IDAN ‘DAYANKU YAYI NUFIN KUSANTAR IYALINSA, TO LALLAI ASAMU ‘DAN AIKE ATSAKANINSU”.

Sai Sahabbai suka ce “Wanne irin ‘dan aike?” Sai yace “SHINE SUMBA (KISS) DA KUMA MUBASHARA (RUNGUMAR JUNA).

Rashin gabatar da irin wadannan wasannin yakan haifar da rashun gamsuwar Jima’i. Shi kuwa rashin gamsuwar Jima’i yakan haifar da matsalolin da zasu kawo rabuwar auren.

Yana daga cikin fa’idodin gabatar da wadannan wasannin, Zai sa Maniyyin ita Macen ya gangaro daga ainihin inda yake, sannan kuma zata samu cikakkiyar gamsuwa.

2. KUSKURE NA BIYU SHINE TSOTSON AL’AURAR JUNA: Mun sha amsa tambayoyi akansa anan Zauren Fiqhu, kuma mun ce wannan kuskure ne babba wanda ko dabbobi basu yinsa. Shi bakin dan Adam anyi masa shi domin yin zikiri ne da karatun Alqur’ani ba wai don Jima’i ba.

Duk da cewa babu wata ayah ko hadisi wanda ya fito Qarara yayi bayani akan haramcin wannan, to amma Malamai sunyi sabani sun kasu gida biyu akan hukuncin yin hakan, Kuma sun raba hukuncin gida biyu:

Idan har yakai ga Shan Maniyyi to Malaman Malikiyyah da Hanafiyyah sun ce HARAMUN ne. Domin su awajensu Maniyyi Najasah ne. Kuma bai halatta Musulmi ya shigar da najasa cikin cikinsa ba.

Idan kuma Maziyyi ne aka tsotsa, to Dukkan Malamai sunce HARAMUN ne. domin kuwa shi Maziyyi najasa ne abisa sa ittifakin Malamai baki daya.

Idan kuma ba’a tsotsi Maziyyi ko maniyyi ba, to Malaman da suke bayar da fatawa a Jami’ar Az’har sunce MAKRUHI NE. Wasu kuma irin su Nasiruddeen Albaniy sunce HARAMUN NE duk da hakan.

3. KUSKURE NA UKU SHINE YAWAITA SURUTAI ALOKACIN JIMA’I : Shima wannan ba daidai bane. Amma ‘Yar magana ka’dan babu laifi sai dai ba’a son cira murya yadda wasu zasu iya jiyowa.

4. KUSKURE NA HUDU SHINE RASHIN LULLUBE JUNA DA MAYAFI: Shima wannan ba daidai bane. yin hakan yayi kama da Jima’in dabbobi kenan.

5. KUSKURE NA BIYAR SHINE RASHIN AMBATON ALLAH KAFIN FARA JIMA’I : Ya kamata Ma’aurata su kula da yin Bismillah tare da karanta addu’ar nan wacce Manzon Allah (saww) yace duk wanda yake karantawa yayin Jima’i da matarsa, to indai aka samu rabo, to shaitan ba zai iya cutar da yaron ba.

Ga addu’ar nan: “BISMILLAHI ALLAHUMMA JANNIBNASH SHAITAN WA JANNIBISH SHAITANA MA RAZAQTANA”.

6. KUSKURE NA SHIDA: idan Miji ya biya bukatarsa, to bai kamata ya gaggauta sauka ba, har sai ita ma matarsa ta biya bukatarta.

7. RASHIN SAUYA YANAYIN KWANCIYAR : Shima wannan ayar Alqur’ani ta bada damar Miji ya sadu da matarsa bisa kowanne irin yanayi. Atsaye ko azaune ko akwance ko atsugunne, mutukar dai ba ta dubura bane.

Don haka ya halatta Ma’aurata su rika chanza yanayin kwanciyarsu saboda Qara ma juna nishadi.

8. KUSKURE NA TAKWAS SHINE SADUWA ALOKACIN DA TAKE CIKIN JININ HAILA, KO JININ HAIHUWA :

Allah (SWT) yace : “SUNA TAMBAYARKA DANGANE DA HAILA, KACE MUSU QAZANTA CE. KU NISANCI MATA ALOKACIN HAILA. KAR KU KUSANCESU HAR SAI SUNYI TSARKI”.

9. KUSKURE NA TARA SHINE SADUWA TA DUBURA: Shima wannan Qazanta ce wacce ko dabbobi basu yi.

Manzon Allah (saww) “TSINANNE NE DUK WANDA YA SADU DA MAI HAILA, KO KUMA YA SADU DA MACE TA DUBURA”.

An kawo wannan ne amatsayin Wa’azantarwa da kuma wayar da kan Ma’aurata. Ba wai da wata manufar ba.

Allah ya ganar damu.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button