Wednesday, 20 March 2019
Kungiyar IZALA tana yin iya kokarinta wajen Ceto Alaramma Ahmad Suleiman

Home Kungiyar IZALA tana yin iya kokarinta wajen Ceto Alaramma Ahmad Suleiman
Ku Tura A Social Media

......Kungiyar tace wasu da ba'a San ko su waye ba, sun fara Neman kudade da sunan za'a karbo su, suna azurta kansu.

Daga Ibrahim Baba Suleiman

Kungiyar wa'azin musulunci ta JIBWIS ta fitar da sanarwa cewa tana iya kokarinta wajen bin duk matakan da suka dace wajen neman masu Garkuwa da mutane sun sako Alaramma Ahmad Suleiman da 'yan tawagarsa. kungiyar tace a daidai wannan lokaci addu'a take bukata daga Al'umma, kuma tana ganin bai kamata ta fito Facebook tana fadin wasu bayanan ba, tunda Abu ne da yake son surru.

Kazalika kungiyar ta samu wasu bayanai daga wasu manya da attajirai cewa akwai wasu da kasuwar su ta bude, suna bi wajen mutane suna neman taimako, wasu suna tura bayani hade da Account No. Na a taimaka da kudade domin ceto su Alaramma, Wadannan mutane ba'a San dasu ba, irin wadanda suke son azurta kansu ne ta haramtasciyar hanya, duk Wanda yazo maka to ka sani cewa ba IZALA ko Iyalan gidan Alaramma Ahmad Suleiman Bane suka turo su.

Shugaban IZALA Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, ya nada Babban kwamiti, karkashin Sheikh Dr. Abdullahi Saleh Pakistan, da Babban Trustee na kungiyar Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina, da Alaramma Nasiru Salihu Gwandu, kuma suna yin duk abun yakamata wajen ceto Alaramma da sauran mutum biyar dake tare da shi.

Kungiyar tace, idan har za'a nemi taimako a wajen mutane, to za'a nemane ta hanyar mutuntawa, ba ta irin hanyar da wadannan bata gari suka fara nema ba.

Haka zalika kungiyar tana Jan hankalin mutane, da su dukufa da addu'oi Allah zai fitar dasu bada jimawa ba insha Allah.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: