Sunday, 10 March 2019
Ko Kasan Tsawon Lokacin Da Ya Kamata Ka Dauka Kana Jima'i Da Matarka?

Home Ko Kasan Tsawon Lokacin Da Ya Kamata Ka Dauka Kana Jima'i Da Matarka?
Ku Tura A Social Media

Daga Tonga Abdul.

Wani abu da yawan mu maza bamu gane ba shi ne yawan lokacin da ya kamata kayi akan matarka a yayi gudanar da jim'i da ita.

Duk da yake babu wani bincike daya tabbatar da hakikanin tsawon lokacin da magidanci zai tsawaita akan matarsa ma'ana yana jima'i da ita, sai dai kuma binciken ya tabbatar da cewa mafi karancin lokacin da namiji zaiyi yana jima'i shi ne daga mintuna  3 zuwa 7, duk namijin da ya kasa daukar wannan lokacin yana saduwa da matarsa to tabbas yana da matsalar daya kamata yaga likita.

Haka zalika mintuna 7 zuwa 13 sune yawan tsawon da idan namiji yayi a lokacin saduwa bai takurawa matarsa ba shi ma bai jigata kansa ba, kamar yadda bincike ya nuna.                                                     

Kamar yadda nazarin ya kara tabbatar da cewa mintuna 10 zuwa 30 akan mace ana jima'i da ita lokuta ne da suka wuce hankali ga maza masu irin wannan jimawan akan matansu, sai dai wadannan tsawon lokutan basu hada da lokutan wasannin motsa sha'awa ba, ana lissafin lokutan ne daga lokacin da shi maigida ya shigar da azzakarinshi cikin mashigar.

Babban abinda ya kamata maza magidanta su kuma fahimta anan shine, ba wai ana nufin cewa dole ne sai maza sun dauki tsawon wadannan lokutan akan matansu ba, ko kuma su takaita kamar yadda binciken ya nuna ba, abin da ya kamata maza su fahinta shine ana bukatar kowane magidanci ya iya fahimtar tsawon lokacin da matarsa take iya samu gamsuwa a jima'ince.

Akwai wasu matan a cikin mintuna biyu kacal sun biya bukata, akwai matan da a lokutan wasannin motsa sha'awa ma sun kawo, kamar yadda ake samun wasu matan muddin ba an dauki sama da sa'a guda ko rabin sa'a ana gurzarsu ba basu san ma ana yi ba.

Don haka ne masana suke bada shawaran cewa, ko wane magidanci dole ne ya fahimci matarsa sosai a jima'ince ta haka ne kawai zai iya gamsar da ita babu cuta babu cutarwa.                   

Abin Lura.

 Gamsar da mace a yayin jima'i dole ne akan dukkannin wani magidanci.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: