Tuesday, 5 March 2019
Idan Gwamnan Bauchi Ya Nemi Sulhu Zamu Daidaita - Inji Nura Hussaini

Home Idan Gwamnan Bauchi Ya Nemi Sulhu Zamu Daidaita - Inji Nura Hussaini
Ku Tura A Social Media

Dan wasan Hausa, Nura Hussaini ya fara ne da cewa "tunda na fara harkar sana'ar Fim, ban taba samun wani cigaban azo a gani ba, har sai da na fara watsa hotunan bidiyon ragargazar manyan mutane.

A lokacin da na saki faifan bidiyo kan dan gidan Gumi  wato Sheikh Ahmed Gumi babu wani jinkiri kai tsaye aka kira ni aka bani kyautar wata tsaleliyar mota anaconda da kuma kimanin naira Miliyan goma.

Shi ma gwamnan Bauchi idan har ya na neman sulhu da ni to ya tuntubi yadda zai gana da ni domin samawa kansa lafiya, in ba haka ba kuwa akwai wasu faya-fayan bidiyon da su ka fi na farko zan saki.

Wata majiya ta sirri ta labarta mana cewa an jiyo Nuran na fadin haka cikin wata zantawa ta sirri da aka jiyo shi ya na yi a wani kebantaccen wuri.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: