Thursday, 7 March 2019
Garabasa Ummi Zeezee Ta sanya Gasar ₦100k Allah yasa A Dace

Home Garabasa Ummi Zeezee Ta sanya Gasar ₦100k Allah yasa A Dace
Ku Tura A Social Media
Tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Zeezee ta saka kacici-kacici inda ta bayyana cewa duk wanda ya lashe zata bashi kyautar kudi naira dubu dari.

Saidai tace sharadin kacici-kacicin shine idan ya kai gobe Juma'a ba'a samu wanda ya lashe ba to ba zata bayar da kudin ba. Abinda Ummi ke so a gayamata shine, shekarunta nawa a Duniya, sannan ran yaushe aka haifeta?

Ta kara da cewa dalilin da yasa ta saka wannan gasa shine saboda mutanen da basu san Asalin shekarunka na Duniya ba amma sai su dinga cema wai ka tsufa dan aci ma mutunci kawai bayan kuma kai kasan har yanzu kai matashine.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: