Wednesday, 20 March 2019
Dalilin da yasa ban goyi bayan kowane dan siyasa ba - Nafis Abdullahi

Home Dalilin da yasa ban goyi bayan kowane dan siyasa ba - Nafis Abdullahi
Ku Tura A Social MediaShahrarriyar jarumar Kannywood, Nafisa Abdullahi, wacce akafi sani da ‘Nafisa Sai Wata Rana’ ta bayyana dalilin da yasa bata yiwa wani dan siyasa yakin neman zaben ba a wannan kakar zaben da ake ciki.

Nafisa Abdullahi ta bayyana cewa ta hana kanta yin hakan ne saboda ba ta son ta tursasa masoyanta zaben wani dan takaran da ba ra'ayinsu ba. Ta fadi wannan magana ne a shafin ra'ayi da sada zumuntarta na Tuwita yayin tattaunawa a daren Lahadi. Nafisa wacce ta fara rayuwar Fim dinta tana shekaru 19 ta amsa tambayar cewa shin meyasa bata bi sauran abokan aikinta wajen yakin neman zabe ga yan siyasa ba, tace:

 "Ban son in canzawa masoya ra'ayinsu kan wanda na zaba. Ina son su zabi dan takaran da suke so." 

Da aka tambayeta shin tana goyon bayan gwamna Abdullahi Umar Ganduje kor Abba Kbari Gida-Gida a zabe zagaye na biyu da zai gudana, tace: "Ba zan iya bayyana hakna a fili ba."

 A baya mun kawo muku cewa daya daga cikin fitattun daraktoci masu ba da umurni a masana'antar Kannywood mai suna Kamal S. Alkali ya roki shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya ginawa 'yan fim din dake arewacin Najeriya gidajen kallo na zamani. Fitaccen daraktan wanda kuma marubuci ne ya yi wannan rokon ne a yayin da yake fira da wakilin majiyar mu inda ya bayyana cewa rashin wuraren kallo kayatattu kuma masu yawa ne yake sa sana'ar ta su ba ta cigaba sosai.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: